ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي

سورة الغاشية - Algashiyah

external-link copy
1 : 88

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡغَٰشِيَةِ

Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka? info
التفاسير:

external-link copy
2 : 88

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ خَٰشِعَةٌ

Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 88

عَامِلَةٞ نَّاصِبَةٞ

Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 88

تَصۡلَىٰ نَارًا حَامِيَةٗ

Zã su shiga wata wuta mai zãfi. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 88

تُسۡقَىٰ مِنۡ عَيۡنٍ ءَانِيَةٖ

Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 88

لَّيۡسَ لَهُمۡ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٖ

Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 88

لَّا يُسۡمِنُ وَلَا يُغۡنِي مِن جُوعٖ

Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 88

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاعِمَةٞ

Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 88

لِّسَعۡيِهَا رَاضِيَةٞ

Game da aikinsu, masu yarda ne. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 88

فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٖ

(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 88

لَّا تَسۡمَعُ فِيهَا لَٰغِيَةٗ

Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 88

فِيهَا عَيۡنٞ جَارِيَةٞ

A cikinta akwai marmaro mai gudãna. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 88

فِيهَا سُرُرٞ مَّرۡفُوعَةٞ

A cikinta akwai gadãje maɗaukaka. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 88

وَأَكۡوَابٞ مَّوۡضُوعَةٞ

Da kõfuna ar'aje. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 88

وَنَمَارِقُ مَصۡفُوفَةٞ

Da filõli* jẽre, info

* Matãsan kai.

التفاسير:

external-link copy
16 : 88

وَزَرَابِيُّ مَبۡثُوثَةٌ

Da katifu shimfiɗe. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 88

أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلۡإِبِلِ كَيۡفَ خُلِقَتۡ

Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su? info
التفاسير:

external-link copy
18 : 88

وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ رُفِعَتۡ

Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta? info
التفاسير:

external-link copy
19 : 88

وَإِلَى ٱلۡجِبَالِ كَيۡفَ نُصِبَتۡ

Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su? info
التفاسير:

external-link copy
20 : 88

وَإِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَيۡفَ سُطِحَتۡ

Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta? info
التفاسير:

external-link copy
21 : 88

فَذَكِّرۡ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٞ

sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 88

لَّسۡتَ عَلَيۡهِم بِمُصَيۡطِرٍ

Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 88

إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ

Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 88

فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَكۡبَرَ

To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 88

إِنَّ إِلَيۡنَآ إِيَابَهُمۡ

Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 88

ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا حِسَابَهُم

Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi. info
التفاسير: