ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي

رقم الصفحة:close

external-link copy
17 : 79

ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ

Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 79

فَقُلۡ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ

"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 79

وَأَهۡدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخۡشَىٰ

"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa?" info
التفاسير:

external-link copy
20 : 79

فَأَرَىٰهُ ٱلۡأٓيَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰ

Sai ya nũna masa ãyar* nan mafi girma. info

* Ãyar Mũsã da ta fi girma ita ce sandarsa mai zama maciji ko hannunsa mai haske kamar tõcila idan yã sanya cikin hammata yã fitar.

التفاسير:

external-link copy
21 : 79

فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ

Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni), info
التفاسير:

external-link copy
22 : 79

ثُمَّ أَدۡبَرَ يَسۡعَىٰ

Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 79

فَحَشَرَ فَنَادَىٰ

Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 79

فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ

Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka." info
التفاسير:

external-link copy
25 : 79

فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلۡأٓخِرَةِ وَٱلۡأُولَىٰٓ

Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 79

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰٓ

Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 79

ءَأَنتُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُۚ بَنَىٰهَا

Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta. info
التفاسير:

external-link copy
28 : 79

رَفَعَ سَمۡكَهَا فَسَوَّىٰهَا

Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 79

وَأَغۡطَشَ لَيۡلَهَا وَأَخۡرَجَ ضُحَىٰهَا

Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 79

وَٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ

Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta. info
التفاسير:

external-link copy
31 : 79

أَخۡرَجَ مِنۡهَا مَآءَهَا وَمَرۡعَىٰهَا

Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 79

وَٱلۡجِبَالَ أَرۡسَىٰهَا

Da duwatsu, Yã kafe ta. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 79

مَتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ

Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 79

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلۡكُبۡرَىٰ

To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 79

يَوۡمَ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا سَعَىٰ

Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 79

وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ

Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 79

فَأَمَّا مَن طَغَىٰ

To, amma wanda ya yi girman kai. info
التفاسير:

external-link copy
38 : 79

وَءَاثَرَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا

Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya). info
التفاسير:

external-link copy
39 : 79

فَإِنَّ ٱلۡجَحِيمَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ

To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 79

وَأَمَّا مَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفۡسَ عَنِ ٱلۡهَوَىٰ

Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai. info
التفاسير:

external-link copy
41 : 79

فَإِنَّ ٱلۡجَنَّةَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ

To, lalle ne Aljanna ita ce makõma. info
التفاسير:

external-link copy
42 : 79

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرۡسَىٰهَا

Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta? info
التفاسير:

external-link copy
43 : 79

فِيمَ أَنتَ مِن ذِكۡرَىٰهَآ

Me ya haɗã ka da ambatonta? info
التفاسير:

external-link copy
44 : 79

إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ

Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake. info
التفاسير:

external-link copy
45 : 79

إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخۡشَىٰهَا

Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta. info
التفاسير:

external-link copy
46 : 79

كَأَنَّهُمۡ يَوۡمَ يَرَوۡنَهَا لَمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا عَشِيَّةً أَوۡ ضُحَىٰهَا

Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa. info
التفاسير: