* Umurnin al'umma da cewa idan sun ga wani al'amari daba su san kansa ba kõ kuwa idan wani abu na ban tsõro ya auku, to, haram ne su yi ta bãrãrarsa domin su firgitar da mutãne. Abin da yake wãjibi a kansu sa'an nan, shi ne su kai rahõtonsa ga shugabanni mãsu sanyãwa a bincika asan yadda abin yake, da kuma yadda zã a yi mãganinsa.
* Umurni zuwa ga Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gareshi.
* Ma'anar ceto: watau wani ya yi wa wani hanya a kan biyan bukãtarsa ta kowace iri, saboda darajar mai yin ceton. Ya kamãta ya yi ceton domin Allah wanda Ya bã shi darajar, bã da ya bai wa Allah kome ba. Idan kuma sayar da ceton yake yi, Allah zai karɓe darajar daga gare shi. Ci da ceto harãmun ne. Sakamakonsa shi ne Allah Ya karɓe darajar ceton daga gare shi.
* A gaisuwa idan an ce muku: "Assalãmu alaikum" ku mayar da cewa, "Wa'alaikumus Salãmu wa rahamatul Lãhi wa barakãtuH." Kõ ku mayar kamar yadda aka yi muku. Watau kada ku naƙasa 'yan'uwanku kõ da ga gaisuwa ne. Faɗakarwa: Fara sallama mustahabbi ne, mayarwa kuma farilla ne, amma wanda ya fãra, ya fi lãda. Haka yin tsarki a gabãnin lokaci mustahabbi ne, amma a bayãn shigar lokaci ya zama wajibi. Wanda ya yi mustahabbi a nan yã fi lãda. Haka jinkirtar da biyan bãshi ga matsattse wãjibine, amma barrantar da shi mustahabbi ne. Yin mustahabbi a nan yã fi lada.