ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي

رقم الصفحة:close

external-link copy
181 : 3

لَّقَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ فَقِيرٞ وَنَحۡنُ أَغۡنِيَآءُۘ سَنَكۡتُبُ مَا قَالُواْ وَقَتۡلَهُمُ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَنَقُولُ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Lalle ne, haƙĩƙa Allah Yã ji maganar waɗanda suka ce: "Lalle ne, Allah faƙĩri ne, mũ ne wadãtattu." za mu rubũta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: "Ku ɗanɗani azãbar gõbara! info
التفاسير:

external-link copy
182 : 3

ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيۡسَ بِظَلَّامٖ لِّلۡعَبِيدِ

"Wannan (azãbar) kuwa sabõda abin da hannuwanku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne Allah bai zama mai zãlunci ga bãyin sa ba." info
التفاسير:

external-link copy
183 : 3

ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ عَهِدَ إِلَيۡنَآ أَلَّا نُؤۡمِنَ لِرَسُولٍ حَتَّىٰ يَأۡتِيَنَا بِقُرۡبَانٖ تَأۡكُلُهُ ٱلنَّارُۗ قُلۡ قَدۡ جَآءَكُمۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِي بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَبِٱلَّذِي قُلۡتُمۡ فَلِمَ قَتَلۡتُمُوهُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah Yã yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi ĩmãni sabõda wani Manzo sai yã zo mana da Baiko wadda wuta za ta ci." Ka ce: "Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabãnĩna, da hujjõji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance mãsu gaskiya?" info
التفاسير:

external-link copy
184 : 3

فَإِن كَذَّبُوكَ فَقَدۡ كُذِّبَ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَ جَآءُو بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُنِيرِ

To, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske. info
التفاسير:

external-link copy
185 : 3

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوۡنَ أُجُورَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ فَمَن زُحۡزِحَ عَنِ ٱلنَّارِ وَأُدۡخِلَ ٱلۡجَنَّةَ فَقَدۡ فَازَۗ وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا مَتَٰعُ ٱلۡغُرُورِ

Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar ¡iyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi. info
التفاسير:

external-link copy
186 : 3

۞ لَتُبۡلَوُنَّ فِيٓ أَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡ وَلَتَسۡمَعُنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَذٗى كَثِيرٗاۚ وَإِن تَصۡبِرُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ذَٰلِكَ مِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

Lalle ne zã a jarraba* ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra. info

* Duk wanda ya tsayu da gaskiya ko umurni da alheri, ko hani daga abin da ba a so, to lalle ne sai an cũtar dashi, kuma ba shi da mãgani sai haƙuri, dõmin Allah, da neman taimako daga Allah, da kõmãwa zuwa ga Allah.

التفاسير: