[1] Akwai daga ni'imõmin Allah,Ya sanya mutum maɗaukaki sabõda addininsa da ĩmãninsa ga Ubangijinsa, kuma Yã bã shi ĩkon binsa da taƙawa kamar yadda Ya yi wa Ibrahĩm. Kuma akwai daga ni'imõmin Allah Ya sanya mutum a cikin zuriyyar mutumin kirki kamar yadda Ya yi wa Annabi Muhammadu Ya sanya shi a cikin zuriyyar Ibrãhĩm.