《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。

Al'waki'ah

external-link copy
1 : 56

إِذَا وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ

Idan mai aukuwa ta auku. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 56

لَيۡسَ لِوَقۡعَتِهَا كَاذِبَةٌ

Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 56

خَافِضَةٞ رَّافِعَةٌ

(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 56

إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجّٗا

Idan aka girgiza ƙasã girgizwa. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 56

وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسّٗا

Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 56

فَكَانَتۡ هَبَآءٗ مُّنۢبَثّٗا

Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 56

وَكُنتُمۡ أَزۡوَٰجٗا ثَلَٰثَةٗ

Kuma kun kasance nau'i uku. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 56

فَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ

Watau mazõwa dãma*. Mẽne ne mazõwa dãma? info

* Mazõwa dãma ko mãsu albarka waɗanda zã a baiwa takardunsu a dãma. Mazõwa hagu ko mãsu shu'umci waɗanda zã a baiwa takardunsu da hagu.

التفاسير:

external-link copy
9 : 56

وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ

Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu? info
التفاسير:

external-link copy
10 : 56

وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلسَّٰبِقُونَ

Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan, info
التفاسير:

external-link copy
11 : 56

أُوْلَٰٓئِكَ ٱلۡمُقَرَّبُونَ

Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 56

فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ

A ckin Aljannar ni'ima. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 56

ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ

Jama'a ne daga mutãnen farko.* info

* Jama'a daga mutãnen farko, sũ ne Annabãwan farko da kaɗan daga cikin mutãnen ƙarshe, shi ne Annabi Muhammadu, sallallãhu alaihi wa sallama. Bã a shiga cikin wannan kashi da aiki sai dai da zãɓin Allah. Kuma an rufe ƙõfarsa. Bãbu sauran wani annabi wanda zai zo da wani addini sãbo a bãyan Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.

التفاسير:

external-link copy
14 : 56

وَقَلِيلٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ

Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 56

عَلَىٰ سُرُرٖ مَّوۡضُونَةٖ

(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 56

مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيۡهَا مُتَقَٰبِلِينَ

Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 56

يَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ

Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 56

بِأَكۡوَابٖ وَأَبَارِيقَ وَكَأۡسٖ مِّن مَّعِينٖ

Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 56

لَّا يُصَدَّعُونَ عَنۡهَا وَلَا يُنزِفُونَ

Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 56

وَفَٰكِهَةٖ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ

Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 56

وَلَحۡمِ طَيۡرٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ

Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 56

وَحُورٌ عِينٞ

Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 56

كَأَمۡثَٰلِ ٱللُّؤۡلُوِٕ ٱلۡمَكۡنُونِ

Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 56

جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 56

لَا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا تَأۡثِيمًا

Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 56

إِلَّا قِيلٗا سَلَٰمٗا سَلَٰمٗا

Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 56

وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ

Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma? info
التفاسير:

external-link copy
28 : 56

فِي سِدۡرٖ مَّخۡضُودٖ

(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 56

وَطَلۡحٖ مَّنضُودٖ

Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 56

وَظِلّٖ مَّمۡدُودٖ

Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya. info
التفاسير:

external-link copy
31 : 56

وَمَآءٖ مَّسۡكُوبٖ

Da wani ruwa mai gudãna. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 56

وَفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ

Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 56

لَّا مَقۡطُوعَةٖ وَلَا مَمۡنُوعَةٖ

Bã su yankẽwa kuma bã a hana su. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 56

وَفُرُشٖ مَّرۡفُوعَةٍ

Da wasu shimfiɗu maɗaukaka. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 56

إِنَّآ أَنشَأۡنَٰهُنَّ إِنشَآءٗ

Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 56

فَجَعَلۡنَٰهُنَّ أَبۡكَارًا

Sa'an nan Muka sanya su budurwai. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 56

عُرُبًا أَتۡرَابٗا

Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya. info
التفاسير:

external-link copy
38 : 56

لِّأَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ

Ga mazõwa dãma. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 56

ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ

Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 56

وَثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ

Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe. info
التفاسير:

external-link copy
41 : 56

وَأَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ

Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu? info
التفاسير:

external-link copy
42 : 56

فِي سَمُومٖ وَحَمِيمٖ

Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi. info
التفاسير:

external-link copy
43 : 56

وَظِلّٖ مِّن يَحۡمُومٖ

Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi. info
التفاسير:

external-link copy
44 : 56

لَّا بَارِدٖ وَلَا كَرِيمٍ

Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba. info
التفاسير:

external-link copy
45 : 56

إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُتۡرَفِينَ

Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi. info
التفاسير:

external-link copy
46 : 56

وَكَانُواْ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلۡحِنثِ ٱلۡعَظِيمِ

Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
47 : 56

وَكَانُواْ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ

Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?" info
التفاسير:

external-link copy
48 : 56

أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ

"Shin, kuma da ubanninmu na farko?" info
التفاسير:

external-link copy
49 : 56

قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَوَّلِينَ وَٱلۡأٓخِرِينَ

Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe." info
التفاسير:

external-link copy
50 : 56

لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ

"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne." info
التفاسير:

external-link copy
51 : 56

ثُمَّ إِنَّكُمۡ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلۡمُكَذِّبُونَ

"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!" info
التفاسير:

external-link copy
52 : 56

لَأٓكِلُونَ مِن شَجَرٖ مِّن زَقُّومٖ

"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)." info
التفاسير:

external-link copy
53 : 56

فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ

"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta." info
التفاسير:

external-link copy
54 : 56

فَشَٰرِبُونَ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡحَمِيمِ

"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi." info
التفاسير:

external-link copy
55 : 56

فَشَٰرِبُونَ شُرۡبَ ٱلۡهِيمِ

"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa." info
التفاسير:

external-link copy
56 : 56

هَٰذَا نُزُلُهُمۡ يَوۡمَ ٱلدِّينِ

Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako. info
التفاسير:

external-link copy
57 : 56

نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ

Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba? info
التفاسير:

external-link copy
58 : 56

أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ

Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi? info
التفاسير:

external-link copy
59 : 56

ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ

Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa? info
التفاسير:

external-link copy
60 : 56

نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ

Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa* ba, info

* Ãyã ta 60 haɗe take da ãya ta 61 watau, bã zã Mu kãsa musanya ku da waɗansu mutãne ba su tsaya matsayinku, sa'an nan kũ kuma Mu mayar da ku wata halitta.

التفاسير:

external-link copy
61 : 56

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ

A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba. info
التفاسير:

external-link copy
62 : 56

وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ

Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba? info
التفاسير:

external-link copy
63 : 56

أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَحۡرُثُونَ

Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa? info
التفاسير:

external-link copy
64 : 56

ءَأَنتُمۡ تَزۡرَعُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلزَّٰرِعُونَ

Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa? info
التفاسير:

external-link copy
65 : 56

لَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَٰهُ حُطَٰمٗا فَظَلۡتُمۡ تَفَكَّهُونَ

Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki. info
التفاسير:

external-link copy
66 : 56

إِنَّا لَمُغۡرَمُونَ

(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!" info
التفاسير:

external-link copy
67 : 56

بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ

"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!" info
التفاسير:

external-link copy
68 : 56

أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلۡمَآءَ ٱلَّذِي تَشۡرَبُونَ

Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha? info
التفاسير:

external-link copy
69 : 56

ءَأَنتُمۡ أَنزَلۡتُمُوهُ مِنَ ٱلۡمُزۡنِ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنزِلُونَ

Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa? info
التفاسير:

external-link copy
70 : 56

لَوۡ نَشَآءُ جَعَلۡنَٰهُ أُجَاجٗا فَلَوۡلَا تَشۡكُرُونَ

Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa? info
التفاسير:

external-link copy
71 : 56

أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي تُورُونَ

Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa? info
التفاسير:

external-link copy
72 : 56

ءَأَنتُمۡ أَنشَأۡتُمۡ شَجَرَتَهَآ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنشِـُٔونَ

Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa? info
التفاسير:

external-link copy
73 : 56

نَحۡنُ جَعَلۡنَٰهَا تَذۡكِرَةٗ وَمَتَٰعٗا لِّلۡمُقۡوِينَ

Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji. info
التفاسير:

external-link copy
74 : 56

فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ

Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
75 : 56

۞ فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ

To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri. info
التفاسير:

external-link copy
76 : 56

وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٞ لَّوۡ تَعۡلَمُونَ عَظِيمٌ

Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani. info
التفاسير:

external-link copy
77 : 56

إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ

Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja. info
التفاسير:

external-link copy
78 : 56

فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ

A cikin wani littafi tsararre. info
التفاسير:

external-link copy
79 : 56

لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ

Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake. info
التفاسير:

external-link copy
80 : 56

تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta. info
التفاسير:

external-link copy
81 : 56

أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ

Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa? info
التفاسير:

external-link copy
82 : 56

وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ

Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)? info
التفاسير:

external-link copy
83 : 56

فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ

To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa). info
التفاسير:

external-link copy
84 : 56

وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ

Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo. info
التفاسير:

external-link copy
85 : 56

وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ

Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani. info
التفاسير:

external-link copy
86 : 56

فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ

To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba? info
التفاسير:

external-link copy
87 : 56

تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.* info

* Idan kun kasance mãsu gaskiya ga da'awar rashin Tãshin Ƙiyãma, to, ku yi ƙõƙarin hana mutuwa ga mutãne dõmin ku hana cikar alkawarin tayarwa a bãyan mutuwa.

التفاسير:

external-link copy
88 : 56

فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ

To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta, info
التفاسير:

external-link copy
89 : 56

فَرَوۡحٞ وَرَيۡحَانٞ وَجَنَّتُ نَعِيمٖ

Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima. info
التفاسير:

external-link copy
90 : 56

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ

Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma, info
التفاسير:

external-link copy
91 : 56

فَسَلَٰمٞ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ

Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma. info
التفاسير:

external-link copy
92 : 56

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ

Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun, info
التفاسير:

external-link copy
93 : 56

فَنُزُلٞ مِّنۡ حَمِيمٖ

Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi. info
التفاسير:

external-link copy
94 : 56

وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ

Da ƙõnuwa da Jahĩm, info
التفاسير:

external-link copy
95 : 56

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ

Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni. info
التفاسير:

external-link copy
96 : 56

فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ

Sabõda haka, ka tsarkake* sũnan Ubangijinka, Mai karimci. info

* A cikin rukũ'i anã tasbĩhi da cewa: "Subhãna Rabbiyal Azĩm wa Bihamdih." Ma'anarsa Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma game da gõde Masa.

التفاسير: