* Ɗãgũtu shi ne dukan mai yin dõkõki waɗanda ba dõkõkin Allah ba. Dukan wanda ya bi dõka wadda ba ta Allah ba a cikin ibãda, ko wadda ta saɓa wa haddin Allah a cikin mu'ãmalõli na haƙƙõƙi ko na laifuka, to, ya shiga cikin wannan tarkon.
* Miyãgun shugabanni mãsu karkatar da mũminai daga hukuncin Allah da hujjar wai suna nufin su daidaita domin a haɗa Musulmi da kãfirai ga hukunci; ta haka har kãfiri ya kasance mai yin hukunci a kan Musulmi. Su waɗannan masu yin haka ba Musulmi ba ne, munãfukan Musulmi ne. Musuluncinsu na bãki ne kawai, dã yã kai ga zũciya dã ba su yi ko tunãnin yarda da haka ba. Allah Ya tsare mu daga sharrin Shaiɗan,.
* Wanda ya ƙi hukuncin Allah, ya yi laifi biyu, domin sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wannan ya nũna rashin ĩmãninsa da Allah da Manzon Sa. Saboda haka ne ãyã mai bin wannan ta ce Musulmi bã su da ĩmãni sai sun yarda da Hukuncin Allah ga kome daga al'amurransu, kuma su yarda da hukuncinsa, bã da jin wani ƙunci a cikin zukatansu ba.