《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。

Yaseen

external-link copy
1 : 36

يسٓ

Y. S̃. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 36

وَٱلۡقُرۡءَانِ ٱلۡحَكِيمِ

Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni* Mai hikima. info

* Al-ƙur'ãni ma'anarsa abin karãtu.

التفاسير:

external-link copy
3 : 36

إِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikin Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 36

عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

A kan hanya madaidaiciya. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 36

تَنزِيلَ ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ

(Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 36

لِتُنذِرَ قَوۡمٗا مَّآ أُنذِرَ ءَابَآؤُهُمۡ فَهُمۡ غَٰفِلُونَ

Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 36

لَقَدۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ عَلَىٰٓ أَكۡثَرِهِمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Lalle, haƙĩƙa, kalma* tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba. info

* Kalma a nan ita ce faɗar Allah da take cewa zai yi azãba ga kãfirin da bai yi ĩmãni ba.

التفاسير:

external-link copy
8 : 36

إِنَّا جَعَلۡنَا فِيٓ أَعۡنَٰقِهِمۡ أَغۡلَٰلٗا فَهِيَ إِلَى ٱلۡأَذۡقَانِ فَهُم مُّقۡمَحُونَ

Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 36

وَجَعَلۡنَا مِنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ سَدّٗا وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ سَدّٗا فَأَغۡشَيۡنَٰهُمۡ فَهُمۡ لَا يُبۡصِرُونَ

Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 36

وَسَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ ءَأَنذَرۡتَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تُنذِرۡهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 36

إِنَّمَا تُنذِرُ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلذِّكۡرَ وَخَشِيَ ٱلرَّحۡمَٰنَ بِٱلۡغَيۡبِۖ فَبَشِّرۡهُ بِمَغۡفِرَةٖ وَأَجۡرٖ كَرِيمٍ

Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 36

إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَنَكۡتُبُ مَا قَدَّمُواْ وَءَاثَٰرَهُمۡۚ وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ فِيٓ إِمَامٖ مُّبِينٖ

Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani. info
التفاسير: