《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。

页码:close

external-link copy
141 : 3

وَلِيُمَحِّصَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَيَمۡحَقَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma dõmin Allah Ya ɗauraye waɗanda suka yi ĩmãni, kuma Ya ƙõƙe kãfirai. info
التفاسير:

external-link copy
142 : 3

أَمۡ حَسِبۡتُمۡ أَن تَدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ وَلَمَّا يَعۡلَمِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ جَٰهَدُواْ مِنكُمۡ وَيَعۡلَمَ ٱلصَّٰبِرِينَ

Ko kun yi zaton ku shiga Aljanna alhãli kuwa Allah bai bãda sanin waɗanda suka yĩ jihãdi daga gare ku ba, kuma Ya san mãsu haƙuri? info
التفاسير:

external-link copy
143 : 3

وَلَقَدۡ كُنتُمۡ تَمَنَّوۡنَ ٱلۡمَوۡتَ مِن قَبۡلِ أَن تَلۡقَوۡهُ فَقَدۡ رَأَيۡتُمُوهُ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ

Kuma lalle ne, haƙĩƙa kun kasance kuna gũrin mutuwa tun a gabãnin ku haɗu da ita, to lalle ne kun gan ta,* alhãli kuwa kuna kallo. info

* Mutuwa watau, kunã gũrin wani yãƙi a bãyan na Badar yã zo.

التفاسير:

external-link copy
144 : 3

وَمَا مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُولٞ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِ ٱلرُّسُلُۚ أَفَإِيْن مَّاتَ أَوۡ قُتِلَ ٱنقَلَبۡتُمۡ عَلَىٰٓ أَعۡقَٰبِكُمۡۚ وَمَن يَنقَلِبۡ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِ فَلَن يَضُرَّ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗاۚ وَسَيَجۡزِي ٱللَّهُ ٱلشَّٰكِرِينَ

Kuma Muhammadu bai zama ba face manzo lalle ne manzanni sun shũɗe a gabãninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, zã kujũya a kan dugaduganku? To, wanda ya jũya a kan dugadugansa, bã zai cũci Allah da kõme ba. Kuma Allah zai sãka wa mãsu gõdiya. info
التفاسير:

external-link copy
145 : 3

وَمَا كَانَ لِنَفۡسٍ أَن تَمُوتَ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِ كِتَٰبٗا مُّؤَجَّلٗاۗ وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَا وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلۡأٓخِرَةِ نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَاۚ وَسَنَجۡزِي ٱلشَّٰكِرِينَ

Kuma bã ya yiwuwa ga wani rai ya mutu fãce da iznin Allah, wa'adi ne mai ƙayyadadden ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon dũniya Muna bã shi daga gare ta. Kuma wanda ke nufin samakon Lãhira Muna bã shi daga gare ta. Kuma zã Mu sãka wa mãsu godiya. info
التفاسير:

external-link copy
146 : 3

وَكَأَيِّن مِّن نَّبِيّٖ قَٰتَلَ مَعَهُۥ رِبِّيُّونَ كَثِيرٞ فَمَا وَهَنُواْ لِمَآ أَصَابَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَمَا ضَعُفُواْ وَمَا ٱسۡتَكَانُواْۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلصَّٰبِرِينَ

Kuma da yawa wani Annabi wanda ya yi yãƙi, akwai jama'a mãsu yawa tãre da shi, sa'an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son mãsu haƙuri. info
التفاسير:

external-link copy
147 : 3

وَمَا كَانَ قَوۡلَهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَإِسۡرَافَنَا فِيٓ أَمۡرِنَا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma bãbu abin da ya kasance maganarsu fãce faɗarsu cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Ka gãfarta mana zunubanmu da ɓarnarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai." info
التفاسير:

external-link copy
148 : 3

فَـَٔاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا وَحُسۡنَ ثَوَابِ ٱلۡأٓخِرَةِۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Allah Yã sãka musu da sakamakon dũniya da kuma kyakkyawan sakamakon Lãhira. Kuma Allah yana son mãsu kyautatãwa. info
التفاسير: