《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。

Al'kahf

external-link copy
1 : 18

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَىٰ عَبۡدِهِ ٱلۡكِتَٰبَ وَلَمۡ يَجۡعَل لَّهُۥ عِوَجَاۜ

Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 18

قَيِّمٗا لِّيُنذِرَ بَأۡسٗا شَدِيدٗا مِّن لَّدُنۡهُ وَيُبَشِّرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرًا حَسَنٗا

Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 18

مَّٰكِثِينَ فِيهِ أَبَدٗا

Sunã mãsu zama a cikinta har abada. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 18

وَيُنذِرَ ٱلَّذِينَ قَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗا

Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda* suka ce: "Allah yanã da ɗa." info

* Lãrabawa sun ce malã'iku 'ya'yan Allah ne. Yahũdawa sunce Uzairu ɗan Allah ne, Nasãra sun ce Ĩsã ɗan Allah ne. Bãbu ladabi ga faɗin wannan magana. Sabõda haka Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gaya musu, cewa wannan magana ƙarya ce kuma rashin ladabi ne ga Allah, da ba su yi ĩmãni ba, ya ji tsõro kada ya zama shĩ ne ya yi ƙwauron bãki ga faɗã musu gaskiya. Sai Allah Ya gaya masa, cewa kada ya halakar da ransa dõmin baƙin cikin haka.

التفاسير: