《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。

页码:close

external-link copy
28 : 17

وَإِمَّا تُعۡرِضَنَّ عَنۡهُمُ ٱبۡتِغَآءَ رَحۡمَةٖ مِّن رَّبِّكَ تَرۡجُوهَا فَقُل لَّهُمۡ قَوۡلٗا مَّيۡسُورٗا

Ko dai ka kau da kai daga gare su dõmin nẽman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fãtanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 17

وَلَا تَجۡعَلۡ يَدَكَ مَغۡلُولَةً إِلَىٰ عُنُقِكَ وَلَا تَبۡسُطۡهَا كُلَّ ٱلۡبَسۡطِ فَتَقۡعُدَ مَلُومٗا مَّحۡسُورًا

Kuma kada ka sanya hannunka ƙuƙuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfiɗa shi dukan shimfiɗãwa har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa.* info

* Kada ka zama marõwaci a zarge ka, kuma kada ka zama almubazzari ka rasa mutãne, su yanke daga gare ka.

التفاسير:

external-link copy
30 : 17

إِنَّ رَبَّكَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Lalle ne Ubangijinka Yanã shimfiɗa arzĩki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntãwa. Lalle Shi, Yã kasance Mai sani ga bãyinSa, Mai gani. info
التفاسير:

external-link copy
31 : 17

وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ خَشۡيَةَ إِمۡلَٰقٖۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُهُمۡ وَإِيَّاكُمۡۚ إِنَّ قَتۡلَهُمۡ كَانَ خِطۡـٔٗا كَبِيرٗا

Kuma kada ku kashe 'yã'yanku dõmin tsõron talauci. Mu ne ke arzũta su, su da ku. Lalle ne kashe su yã kasance kuskure babba. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 17

وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلزِّنَىٰٓۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَسَآءَ سَبِيلٗا

Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 17

وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَمَن قُتِلَ مَظۡلُومٗا فَقَدۡ جَعَلۡنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلۡطَٰنٗا فَلَا يُسۡرِف فِّي ٱلۡقَتۡلِۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورٗا

Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 17

وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ بِٱلۡعَهۡدِۖ إِنَّ ٱلۡعَهۡدَ كَانَ مَسۡـُٔولٗا

Kuma kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce dai da sifa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yã kasance abin tambayãwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 17

وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ إِذَا كِلۡتُمۡ وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلٗا

Kuma ku cika mũdu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikẽli madaidaici. Wancan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 17

وَلَا تَقۡفُ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَٰٓئِكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولٗا

Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 17

وَلَا تَمۡشِ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَحًاۖ إِنَّكَ لَن تَخۡرِقَ ٱلۡأَرۡضَ وَلَن تَبۡلُغَ ٱلۡجِبَالَ طُولٗا

Kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa da alfahari. Lalle kai bã zã ka hũda ƙasa ba kuma bã zã ka kai a duwãtsu ba ga tsawo. info
التفاسير:

external-link copy
38 : 17

كُلُّ ذَٰلِكَ كَانَ سَيِّئُهُۥ عِندَ رَبِّكَ مَكۡرُوهٗا

Dukan wancan mli mũninsa yã kasance abin ƙyãma a wurin Ubangijin ka. info
التفاسير: