《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。

Al'adiyat

external-link copy
1 : 100

وَٱلۡعَٰدِيَٰتِ ضَبۡحٗا

Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 100

فَٱلۡمُورِيَٰتِ قَدۡحٗا

Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 100

فَٱلۡمُغِيرَٰتِ صُبۡحٗا

Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 100

فَأَثَرۡنَ بِهِۦ نَقۡعٗا

Sai su motsar da ƙũra game da shi. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 100

فَوَسَطۡنَ بِهِۦ جَمۡعًا

Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 100

إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٞ

Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 100

وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٞ

Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 100

وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلۡخَيۡرِ لَشَدِيدٌ

Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 100

۞ أَفَلَا يَعۡلَمُ إِذَا بُعۡثِرَ مَا فِي ٱلۡقُبُورِ

Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 100

وَحُصِّلَ مَا فِي ٱلصُّدُورِ

Aka bayyana abin da ke cikin zukata. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 100

إِنَّ رَبَّهُم بِهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّخَبِيرُۢ

Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne? info
التفاسير: