Salin ng mga Kahulugan ng Marangal na Qur'an - Salin sa Wikang Hausa ni Abubakr Gumi

Numero ng Pahina:close

external-link copy
60 : 6

وَهُوَ ٱلَّذِي يَتَوَفَّىٰكُم بِٱلَّيۡلِ وَيَعۡلَمُ مَا جَرَحۡتُم بِٱلنَّهَارِ ثُمَّ يَبۡعَثُكُمۡ فِيهِ لِيُقۡضَىٰٓ أَجَلٞ مُّسَمّٗىۖ ثُمَّ إِلَيۡهِ مَرۡجِعُكُمۡ ثُمَّ يُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar* rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. info

* Karɓar rai da dare dõmin barci, tãyarwa a cikin ranã, watau yini daga barci. Akwai misalta dare da dũniya kuma rãna da Rãnar Ƙiyãma, kuma mutuwa da barci, da farkawa daga barci da Tãshin Ƙiyãma. Ãyar tã ƙunsa asĩrai mãsu yawa.

التفاسير:

external-link copy
61 : 6

وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۖ وَيُرۡسِلُ عَلَيۡكُمۡ حَفَظَةً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ تَوَفَّتۡهُ رُسُلُنَا وَهُمۡ لَا يُفَرِّطُونَ

Kuma Shĩ ne Mai rinjãya bisa ga bãyinSa, kuma Yanã aikan mãsu tsaro a kanku, har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayanku, sai manzannin Mu su karɓi ransa alhãli su ba su yin sakaci. info
التفاسير:

external-link copy
62 : 6

ثُمَّ رُدُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ مَوۡلَىٰهُمُ ٱلۡحَقِّۚ أَلَا لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَهُوَ أَسۡرَعُ ٱلۡحَٰسِبِينَ

Sa'an nan kuma a mayar da su zuwa ga Allah Ubangjinsu na gaskiya. To! A gare shi hukunci yake, kuma Shi ne Mafi gaugãwar mãsu bincike. info
التفاسير:

external-link copy
63 : 6

قُلۡ مَن يُنَجِّيكُم مِّن ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ تَدۡعُونَهُۥ تَضَرُّعٗا وَخُفۡيَةٗ لَّئِنۡ أَنجَىٰنَا مِنۡ هَٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّٰكِرِينَ

Ka ce: "Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kunã kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓõye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan (masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga mãsu gõdiya?'" info
التفاسير:

external-link copy
64 : 6

قُلِ ٱللَّهُ يُنَجِّيكُم مِّنۡهَا وَمِن كُلِّ كَرۡبٖ ثُمَّ أَنتُمۡ تُشۡرِكُونَ

Ka ce: "Allah ne Yake tsĩrar da ku daga gare ta, kuma daga dukan baƙin ciki sa'an nan kuma ku, kunã yin shirki!" info
التفاسير:

external-link copy
65 : 6

قُلۡ هُوَ ٱلۡقَادِرُ عَلَىٰٓ أَن يَبۡعَثَ عَلَيۡكُمۡ عَذَابٗا مِّن فَوۡقِكُمۡ أَوۡ مِن تَحۡتِ أَرۡجُلِكُمۡ أَوۡ يَلۡبِسَكُمۡ شِيَعٗا وَيُذِيقَ بَعۡضَكُم بَأۡسَ بَعۡضٍۗ ٱنظُرۡ كَيۡفَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَفۡقَهُونَ

Ka ce: "Shĩ ne Mai ĩko a kan Ya aika da wata azãba a kanku daga bisanku, kõ kuwa daga ƙarƙashin ƙafãfunku, kõ kuwa Ya gauraya ku ƙungiyõyi, kuma Ya ɗanɗanã wa sãshenku masĩfar sãshe." "Ka dũba yadda Muke sarrafa ãyõyi, tsammãninsu sunã fahimta!" info
التفاسير:

external-link copy
66 : 6

وَكَذَّبَ بِهِۦ قَوۡمُكَ وَهُوَ ٱلۡحَقُّۚ قُل لَّسۡتُ عَلَيۡكُم بِوَكِيلٖ

Kuma mutãnenka sun ƙaryata (ka) game da Shi, alhãli kuwa Shi ne gaskiya. Ka ce: "Nĩban zama wakĩli a kanku ba." info
التفاسير:

external-link copy
67 : 6

لِّكُلِّ نَبَإٖ مُّسۡتَقَرّٞۚ وَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

"Akwai matabbata ga dukan lãbãri, kuma zã ku sani." info
التفاسير:

external-link copy
68 : 6

وَإِذَا رَأَيۡتَ ٱلَّذِينَ يَخُوضُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيۡرِهِۦۚ وَإِمَّا يُنسِيَنَّكَ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَلَا تَقۡعُدۡ بَعۡدَ ٱلذِّكۡرَىٰ مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ

Kuma idan kã ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kũtsa a cikin wani lãbãri waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunãwa tãre da mutãne azzãlumai. info
التفاسير: