Salin ng mga Kahulugan ng Marangal na Qur'an - Salin sa Wikang Hausa ni Abubakr Gumi

Numero ng Pahina:close

external-link copy
141 : 4

ٱلَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمۡ فَإِن كَانَ لَكُمۡ فَتۡحٞ مِّنَ ٱللَّهِ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَكُن مَّعَكُمۡ وَإِن كَانَ لِلۡكَٰفِرِينَ نَصِيبٞ قَالُوٓاْ أَلَمۡ نَسۡتَحۡوِذۡ عَلَيۡكُمۡ وَنَمۡنَعۡكُم مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ فَٱللَّهُ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَلَن يَجۡعَلَ ٱللَّهُ لِلۡكَٰفِرِينَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ سَبِيلًا

Waɗanda suke jiran dãko game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: "Ashe, ba mu kasance tãre da kũ ba?" Kuma idan wani rabo ya sãmu ga kãfirai sai su ce: "Ashe ba mu rinjãye ku ba, kuma muka tsare ku daga mũminai?" To, Allah ne Yake yin hukunci tsakãninku a Rãnar ¡iyãma, kuma Allah bã zai sanya hanya ba ga kãfirai a kan mũminai. info
التفاسير:

external-link copy
142 : 4

إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ يُخَٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَهُوَ خَٰدِعُهُمۡ وَإِذَا قَامُوٓاْ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ قَامُواْ كُسَالَىٰ يُرَآءُونَ ٱلنَّاسَ وَلَا يَذۡكُرُونَ ٱللَّهَ إِلَّا قَلِيلٗا

Lalle ne munãfukai sunã yaudarẽwa da Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga salla, sai su tãshi sunã mãsu kasãla. Suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan. info
التفاسير:

external-link copy
143 : 4

مُّذَبۡذَبِينَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ لَآ إِلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِ وَلَآ إِلَىٰ هَٰٓؤُلَآءِۚ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ سَبِيلٗا

Mãsu kai-kawo ne a tsakãnin wancan; bã zuwa ga waɗannan ba, kuma bã zuwa ga waɗannan ba. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã za ka sãmar masa wata Hanya ba. info
التفاسير:

external-link copy
144 : 4

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ عَلَيۡكُمۡ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينًا

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin, kanã nufin ku sanyã wa Allah dalĩli bayyananne a kanku? info
التفاسير:

external-link copy
145 : 4

إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِي ٱلدَّرۡكِ ٱلۡأَسۡفَلِ مِنَ ٱلنَّارِ وَلَن تَجِدَ لَهُمۡ نَصِيرًا

Lalle ne, manãfukai sunã a magangara mafi ƙasƙanci daga wuta. Kuma bã zã ka sãma musu mataimaki ba. info
التفاسير:

external-link copy
146 : 4

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَٱعۡتَصَمُواْ بِٱللَّهِ وَأَخۡلَصُواْ دِينَهُمۡ لِلَّهِ فَأُوْلَٰٓئِكَ مَعَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَسَوۡفَ يُؤۡتِ ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَجۡرًا عَظِيمٗا

Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka nẽmi fakuwa ga Allah, kuma suka tsarkake addininsu dõmin Allah, to, waɗannan sunã tãre da mũminai, kuma Allah zai bai wa mũminai lãda mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
147 : 4

مَّا يَفۡعَلُ ٱللَّهُ بِعَذَابِكُمۡ إِن شَكَرۡتُمۡ وَءَامَنتُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ شَاكِرًا عَلِيمٗا

Mẽne ne Allah zai amfãna da yi maku azãba idan kun gõde, kuma kun yi ĩmãni? Allah Yã ksance Mai gõdiya Masani. info
التفاسير: