పవిత్ర ఖురాన్ యొక్క భావార్థాల అనువాదం - హౌసా అనువాదం - అబూ బక్ర్ జూమీ

Almursala

external-link copy
1 : 77

وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا

Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 77

فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا

Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 77

وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا

Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 77

فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا

sa'an nan, da ãyõyi* mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa. info

* Yã kamanta Manzanin Allah masu kãwo ayõyinsa da iskõki mãsu kãwo ruwa dõmin rahamar da ke cikin kowannensu.

التفاسير:

external-link copy
5 : 77

فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا

Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 77

عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا

Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 77

إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٞ

Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne info
التفاسير:

external-link copy
8 : 77

فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ

To, idan taurãri aka shãfe haskensu. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 77

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ

Kuma, idan sama aka tsãge ta. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 77

وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ

Kuma, idan duwãtsu aka nike su. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 77

وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ

Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 77

لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ

Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 77

لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ

Domin rãnar rarrabẽwa.* info

* Yin hukunci a tsakanin tãlikai.

التفاسير:

external-link copy
14 : 77

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ

Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa? info
التفاسير:

external-link copy
15 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
16 : 77

أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِينَ

Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 77

ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡأٓخِرِينَ

Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe? info
التفاسير:

external-link copy
18 : 77

كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ

Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
20 : 77

أَلَمۡ نَخۡلُقكُّم مِّن مَّآءٖ مَّهِينٖ

Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 77

فَجَعَلۡنَٰهُ فِي قَرَارٖ مَّكِينٍ

Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 77

إِلَىٰ قَدَرٖ مَّعۡلُومٖ

Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 77

فَقَدَرۡنَا فَنِعۡمَ ٱلۡقَٰدِرُونَ

Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
25 : 77

أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا

Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 77

أَحۡيَآءٗ وَأَمۡوَٰتٗا

Ga rãyayyu da matattu, info
التفاسير:

external-link copy
27 : 77

وَجَعَلۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ شَٰمِخَٰتٖ وَأَسۡقَيۡنَٰكُم مَّآءٗ فُرَاتٗا

Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi? info
التفاسير:

external-link copy
28 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
29 : 77

ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ

Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi! info
التفاسير:

external-link copy
30 : 77

ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ ظِلّٖ ذِي ثَلَٰثِ شُعَبٖ

Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku. info
التفاسير:

external-link copy
31 : 77

لَّا ظَلِيلٖ وَلَا يُغۡنِي مِنَ ٱللَّهَبِ

Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 77

إِنَّهَا تَرۡمِي بِشَرَرٖ كَٱلۡقَصۡرِ

Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 77

كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٞ صُفۡرٞ

Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
35 : 77

هَٰذَا يَوۡمُ لَا يَنطِقُونَ

Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 77

وَلَا يُؤۡذَنُ لَهُمۡ فَيَعۡتَذِرُونَ

Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
38 : 77

هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِۖ جَمَعۡنَٰكُمۡ وَٱلۡأَوَّلِينَ

Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 77

فَإِن كَانَ لَكُمۡ كَيۡدٞ فَكِيدُونِ

To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
41 : 77

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي ظِلَٰلٖ وَعُيُونٖ

Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari. info
التفاسير:

external-link copy
42 : 77

وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشۡتَهُونَ

Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari. info
التفاسير:

external-link copy
43 : 77

كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa." info
التفاسير:

external-link copy
44 : 77

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
45 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
46 : 77

كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ

(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne." info
التفاسير:

external-link copy
47 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
48 : 77

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا يَرۡكَعُونَ

Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba." info
التفاسير:

external-link copy
49 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
50 : 77

فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ

To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni info
التفاسير: