* Wanda yake rantsuwar alkawari da wani, sa'an nan ya warware rantsuwar dõmin neman ya ƙulla wata rantsuwa da wani mutum sabõda wani amfãninsa kõ jama'arsa a cikin wata kabĩla wadda ta fi ta mutãnen farko ƙarfi to, siffarsa kamar mace ce mahaukaciya, mai yin zare, a bayan ta tukka shi, ya yi ƙarfi, sa'an nan ta warware shi. Sabõda haka idan ta so mayar da shi wani zare, to, bã zai yi kyau ba kamar zaren farko da ta yi kuma mutãne sun gãne haukarta, bã zã su yi wata ma'ãmala da ita ba. Wanda ya yi rantsuwa da Allah a kan abu, to, yã sanya Allah lãmuni ke nan. Bã ya halatta ga wanda ya shugabantar da Allah ga wani abu, sa'an nan ya kõma bãya ya ƙi cika wannan alkawarin dõmin bai kiyãye girman Allah ba, wanda ya sanya a tsakaninsa da abõkin ma'ãmalarsa. Tsaron alkawari ni'ima ne.