அல்குர்ஆன் மொழிபெயர்ப்பு - ஹவுஸா மொழிபெயர்ப்பு - அபூபக்கர் ஜுமி

Al'alaq

external-link copy
1 : 96

ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 96

خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِنۡ عَلَقٍ

Ya hahitta mutum daga gudan jini. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 96

ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ

Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 96

ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ

Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 96

عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ

Ya sanar da mutum abin da bai sani ba. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 96

كَلَّآ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَيَطۡغَىٰٓ

A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu). info
التفاسير:

external-link copy
7 : 96

أَن رَّءَاهُ ٱسۡتَغۡنَىٰٓ

Dõmin yã ga kansa, yã wadãta. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 96

إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجۡعَىٰٓ

Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 96

أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يَنۡهَىٰ

Shin, kã ga wanda ke hana. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 96

عَبۡدًا إِذَا صَلَّىٰٓ

Bãwã idan yã yi salla? info
التفاسير:

external-link copy
11 : 96

أَرَءَيۡتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلۡهُدَىٰٓ

Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya? info
التفاسير:

external-link copy
12 : 96

أَوۡ أَمَرَ بِٱلتَّقۡوَىٰٓ

Ko ya yi umurni da taƙawa? info
التفاسير:

external-link copy
13 : 96

أَرَءَيۡتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ

Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya? info
التفاسير:

external-link copy
14 : 96

أَلَمۡ يَعۡلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ

Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani? info
التفاسير:

external-link copy
15 : 96

كَلَّا لَئِن لَّمۡ يَنتَهِ لَنَسۡفَعَۢا بِٱلنَّاصِيَةِ

A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 96

نَاصِيَةٖ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةٖ

Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 96

فَلۡيَدۡعُ نَادِيَهُۥ

Sai ya kirayi ƙungiyarsa. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 96

سَنَدۡعُ ٱلزَّبَانِيَةَ

Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma). info
التفاسير:

external-link copy
19 : 96

كَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡۤ وَٱقۡتَرِب۩

A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka). info

* Wato salla da sauran ibãdu.

التفاسير: