அல்குர்ஆன் மொழிபெயர்ப்பு - ஹவுஸா மொழிபெயர்ப்பு - அபூபக்கர் ஜுமி

பக்க எண்:close

external-link copy
34 : 40

وَلَقَدۡ جَآءَكُمۡ يُوسُفُ مِن قَبۡلُ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَمَا زِلۡتُمۡ فِي شَكّٖ مِّمَّا جَآءَكُم بِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَا هَلَكَ قُلۡتُمۡ لَن يَبۡعَثَ ٱللَّهُ مِنۢ بَعۡدِهِۦ رَسُولٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَنۡ هُوَ مُسۡرِفٞ مُّرۡتَابٌ

"Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da ya halaka kuka ce, 'Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa.' Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka." info
التفاسير:

external-link copy
35 : 40

ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ سُلۡطَٰنٍ أَتَىٰهُمۡۖ كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ وَعِندَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ قَلۡبِ مُتَكَبِّرٖ جَبَّارٖ

"Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai tĩlastãwa." info
التفاسير:

external-link copy
36 : 40

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَٰهَٰمَٰنُ ٱبۡنِ لِي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَبۡلُغُ ٱلۡأَسۡبَٰبَ

Kuma Fir'auna ye ce, "Yã Hãmana! Ka gina mini bẽne, dammãnĩna zã ni isa ga ƙõfõfi." info
التفاسير:

external-link copy
37 : 40

أَسۡبَٰبَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ فَأَطَّلِعَ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ كَٰذِبٗاۚ وَكَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِفِرۡعَوۡنَ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَصُدَّ عَنِ ٱلسَّبِيلِۚ وَمَا كَيۡدُ فِرۡعَوۡنَ إِلَّا فِي تَبَابٖ

"¡õfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci." Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir'auna mũnãnan aikinsa kuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama ba fãce yanã a cikin hasãra." info
التفاسير:

external-link copy
38 : 40

وَقَالَ ٱلَّذِيٓ ءَامَنَ يَٰقَوۡمِ ٱتَّبِعُونِ أَهۡدِكُمۡ سَبِيلَ ٱلرَّشَادِ

Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bĩ ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa." info
التفاسير:

external-link copy
39 : 40

يَٰقَوۡمِ إِنَّمَا هَٰذِهِ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا مَتَٰعٞ وَإِنَّ ٱلۡأٓخِرَةَ هِيَ دَارُ ٱلۡقَرَارِ

"Kuma ya mutãnẽna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata." info
التفاسير:

external-link copy
40 : 40

مَنۡ عَمِلَ سَيِّئَةٗ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَاۖ وَمَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ يُرۡزَقُونَ فِيهَا بِغَيۡرِ حِسَابٖ

"Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba." info
التفاسير: