* Mãtar Imrãna sunanta Hannatu ɗiyar fãƙũza, bã ta haifuwa, sai wata rãna ta ga tsuntsuwa tanã ciyar da tsãkonta, sai ta yi sha'awar sãmun ɗa sabõda haka ta rõki Allah Ya bã ta ɗa. Da mijinta Imrãna ya tãke ta sai ta sãmi ciki, dõmin murna sai ta yi alkwarin 'yanta shi da bakance ga Masallacin Baitil Muƙaddas dõmin ya riƙa yi masa hidima. To, a lõkacin da ta haihu sai ta sãmi ɗiya mace. Ga shari'arsu bã a 'yanta mace ga irin wannan aiki na hidimar masallaci, dõmin haka ta nemi uzuri da cewa ta haife ta mace, mace bã kamar namiji take ba. Har ta yi ruɗu ta jũya, ta ce, namijin bã kamar mace ba, dõmin namiji ne a cikin zũciyarta.
* Maryam, ma'anarta mai ibãda. Abinci da ake kai mata a cikin Masallaci shĩ ne 'ya'yan itãce, irin na ɗãri, a lõkacin bazara, kuma irin na bazara a lõkacin ɗãri. Wannan kuma ya mõtsar da begen zakariyya ga sãmun ɗã, bãyan shi da mãtarsa sun tsũfa ba su haifu ba. Sai ya rõƙi Allah kuma Ya karɓa masa, Ya ba shi Yahaya Annabi.