அல்குர்ஆன் மொழிபெயர்ப்பு - ஹவுஸா மொழிபெயர்ப்பு - அபூபக்கர் ஜுமி

external-link copy
67 : 16

وَمِن ثَمَرَٰتِ ٱلنَّخِيلِ وَٱلۡأَعۡنَٰبِ تَتَّخِذُونَ مِنۡهُ سَكَرٗا وَرِزۡقًا حَسَنًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye* da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta. info

* Yã ambaci abin mãye a cikin abũbuwan ni'ima a gabãnin aharamta giya. Kuma haramtã ta bã ya hanã ta zuma a cikin ni'imõmin Allah ga mutãne dõmin an haramtã ne sabõda tsaron hankalinmu a kan neman waɗansu ni'imõmin da suka fĩ ta a Aljanna a inda bã zã a hana ta ba sabõda ƙarewar taklĩfi a can. Sabõda haka ne ya ƙãre ãyar da cewa: "Akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.".

التفاسير: