அல்குர்ஆன் மொழிபெயர்ப்பு - ஹவுஸா மொழிபெயர்ப்பு - அபூபக்கர் ஜுமி

Yusuf

external-link copy
1 : 12

الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 12

إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 12

نَحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ أَحۡسَنَ ٱلۡقَصَصِ بِمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ وَإِن كُنتَ مِن قَبۡلِهِۦ لَمِنَ ٱلۡغَٰفِلِينَ

Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 12

إِذۡ قَالَ يُوسُفُ لِأَبِيهِ يَٰٓأَبَتِ إِنِّي رَأَيۡتُ أَحَدَ عَشَرَ كَوۡكَبٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ رَأَيۡتُهُمۡ لِي سَٰجِدِينَ

A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni." info
التفاسير: