د قرآن کریم د معناګانو ژباړه - هوساوي ژباړه - ابو بکر ګومي

Almursala

external-link copy
1 : 77

وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا

Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 77

فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا

Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 77

وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا

Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 77

فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا

sa'an nan, da ãyõyi* mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa. info

* Yã kamanta Manzanin Allah masu kãwo ayõyinsa da iskõki mãsu kãwo ruwa dõmin rahamar da ke cikin kowannensu.

التفاسير:

external-link copy
5 : 77

فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا

Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 77

عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا

Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 77

إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٞ

Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne info
التفاسير:

external-link copy
8 : 77

فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ

To, idan taurãri aka shãfe haskensu. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 77

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ

Kuma, idan sama aka tsãge ta. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 77

وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ

Kuma, idan duwãtsu aka nike su. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 77

وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ

Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 77

لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ

Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 77

لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ

Domin rãnar rarrabẽwa.* info

* Yin hukunci a tsakanin tãlikai.

التفاسير:

external-link copy
14 : 77

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ

Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa? info
التفاسير:

external-link copy
15 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
16 : 77

أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِينَ

Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 77

ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡأٓخِرِينَ

Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe? info
التفاسير:

external-link copy
18 : 77

كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ

Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 77

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! info
التفاسير: