د قرآن کریم د معناګانو ژباړه - هوساوي ژباړه - ابو بکر ګومي

Alkiyama

external-link copy
1 : 75

لَآ أُقۡسِمُ بِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ

Bã sai Nã yi rantsuwa* da Rãnar ¡iyãma ba. info

* Wasu na fassarawa: lna rantsuwa da Rãnar Ƙiyama. A ganina, da tabbatar da rantsuwar da kuma kore ta duka ɗaya ne, maƙasũdi dai jan hankalin mai karãtu ga abin da yake a ciki, na hikimar Allah.

التفاسير:

external-link copy
2 : 75

وَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلنَّفۡسِ ٱللَّوَّامَةِ

Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin* kansa ba. info

* Kowane rai na zargin kansa idan bai yi aikin alheri ba, ko kuma bai yi fiye da wanda ya yi ba, ko kuma bai aikata wanda ya fi kyãwo ba a lokacin aikinsa.

التفاسير:

external-link copy
3 : 75

أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ

Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba? info
التفاسير:

external-link copy
4 : 75

بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ

Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 75

بَلۡ يُرِيدُ ٱلۡإِنسَٰنُ لِيَفۡجُرَ أَمَامَهُۥ

Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 75

يَسۡـَٔلُ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلۡقِيَٰمَةِ

Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?" info
التفاسير:

external-link copy
7 : 75

فَإِذَا بَرِقَ ٱلۡبَصَرُ

To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli). info
التفاسير:

external-link copy
8 : 75

وَخَسَفَ ٱلۡقَمَرُ

Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe). info
التفاسير:

external-link copy
9 : 75

وَجُمِعَ ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ

Aka tãra rãnã da watã info
التفاسير:

external-link copy
10 : 75

يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ

Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?" info
التفاسير:

external-link copy
11 : 75

كَلَّا لَا وَزَرَ

A'aha! bãbu mafaka. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 75

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ

zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 75

يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ

Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 75

بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٞ

Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 75

وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ

Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba). info
التفاسير:

external-link copy
16 : 75

لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ

Kada ka mõtsar* da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni). info

* Dangantakar wannan ãya da ta sama da ita, ita ce bambancin Annabi mai gaggawar karɓar umurnin Allah da ƙyamar kãfiri ga karɓarsa, da bayãnin sauƙaƙewar Allah ga mai bin umurninSa.

التفاسير:

external-link copy
17 : 75

إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ

Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 75

فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ

To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 75

ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ

sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 75

كَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ

A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 75

وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ

Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira). info
التفاسير:

external-link copy
22 : 75

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاضِرَةٌ

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 75

إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٞ

Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 75

وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٞ

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 75

تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٞ

Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 75

كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ

A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 75

وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٖ

kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?" info
التفاسير:

external-link copy
28 : 75

وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ

Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 75

وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ

Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 75

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ

Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa* take. info

* Ranar kora mutane, kamar ana gargaɗa tumãki, zuwa ga tsayuwa a gaba ga Allah, dõmin hisabi.

التفاسير:

external-link copy
31 : 75

فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ

To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba! info
التفاسير:

external-link copy
32 : 75

وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ

Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya! info
التفاسير:

external-link copy
33 : 75

ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ

Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 75

أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰ

Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 75

ثُمَّ أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰٓ

Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 75

أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَن يُتۡرَكَ سُدًى

Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)? info
التفاسير:

external-link copy
37 : 75

أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةٗ مِّن مَّنِيّٖ يُمۡنَىٰ

Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa) info
التفاسير:

external-link copy
38 : 75

ثُمَّ كَانَ عَلَقَةٗ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ

Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa; info
التفاسير:

external-link copy
39 : 75

فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ

Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace? info
التفاسير:

external-link copy
40 : 75

أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ

Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?* info

* Ana son mai karãtu a nan ya ce: a ɓoye بلى وأنا على ذلك من الشاهدين.

التفاسير: