د قرآن کریم د معناګانو ژباړه - هوساوي ژباړه - ابو بکر ګومي

د مخ نمبر:close

external-link copy
41 : 40

۞ وَيَٰقَوۡمِ مَا لِيٓ أَدۡعُوكُمۡ إِلَى ٱلنَّجَوٰةِ وَتَدۡعُونَنِيٓ إِلَى ٱلنَّارِ

"Kuma ya mutãnẽna! Me ya sãme ni, inã kiran ku zuwa ga tsĩra, kuma kunã kira na zuwa ga wutã?" info
التفاسير:

external-link copy
42 : 40

تَدۡعُونَنِي لِأَكۡفُرَ بِٱللَّهِ وَأُشۡرِكَ بِهِۦ مَا لَيۡسَ لِي بِهِۦ عِلۡمٞ وَأَنَا۠ أَدۡعُوكُمۡ إِلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡغَفَّٰرِ

"Kuna kira na zuwa ga in kãfirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da abin da bãbu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni inã kiran ku zuwa ga Mabuwãyi, Mai gãfara." info
التفاسير:

external-link copy
43 : 40

لَا جَرَمَ أَنَّمَا تَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِ لَيۡسَ لَهُۥ دَعۡوَةٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَلَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ مَرَدَّنَآ إِلَى ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ

"Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, bã ya da wani kira a cikin dũniya, kuma bã shi da shi a Lãhira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take, kuma lalle mabarnata sũ ne 'yan wutã." info
التفاسير:

external-link copy
44 : 40

فَسَتَذۡكُرُونَ مَآ أَقُولُ لَكُمۡۚ وَأُفَوِّضُ أَمۡرِيٓ إِلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ

"To zã ku ambaci abin da nake gaya muku, kuma inã fawwala al'amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai gani ne ga bãyin Sa." info
التفاسير:

external-link copy
45 : 40

فَوَقَىٰهُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِ مَا مَكَرُواْۖ وَحَاقَ بِـَٔالِ فِرۡعَوۡنَ سُوٓءُ ٱلۡعَذَابِ

Sai Allah Ya tsare shi daga mũnãnan abũbuwa da suka yi na mãkirci, kuma mummunar azãba ta wajaba ga mutãnen Fir'auna. info
التفاسير:

external-link copy
46 : 40

ٱلنَّارُ يُعۡرَضُونَ عَلَيۡهَا غُدُوّٗا وَعَشِيّٗاۚ وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ أَدۡخِلُوٓاْ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ أَشَدَّ ٱلۡعَذَابِ

Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, "Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba." info
التفاسير:

external-link copy
47 : 40

وَإِذۡ يَتَحَآجُّونَ فِي ٱلنَّارِ فَيَقُولُ ٱلضُّعَفَٰٓؤُاْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا كُنَّا لَكُمۡ تَبَعٗا فَهَلۡ أَنتُم مُّغۡنُونَ عَنَّا نَصِيبٗا مِّنَ ٱلنَّارِ

Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna (mabiya) su ce wa waɗanda suka kangara (shugabanni), "Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to, shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã?" info
التفاسير:

external-link copy
48 : 40

قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُوٓاْ إِنَّا كُلّٞ فِيهَآ إِنَّ ٱللَّهَ قَدۡ حَكَمَ بَيۡنَ ٱلۡعِبَادِ

Waɗanda suka kangara suka ce: "Lalle mũ duka munã a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakãnin bãyin Sa." info
التفاسير:

external-link copy
49 : 40

وَقَالَ ٱلَّذِينَ فِي ٱلنَّارِ لِخَزَنَةِ جَهَنَّمَ ٱدۡعُواْ رَبَّكُمۡ يُخَفِّفۡ عَنَّا يَوۡمٗا مِّنَ ٱلۡعَذَابِ

Kuma waɗanda suke a cikin wutã suka ce wa matsaran Jahannama, "Ku rõki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana, a yini ɗaya, daga azãba." info
التفاسير: