* An ruwaito cewa Allah Ya bũɗe musu ƙõfar Jahannama, zãfi ya hana su zama akõ'ina cikin gidãjensu, sa'an nan aka sanya girgije ya yi musu inuwa mai sanyi-sanyi har suka tãru a ciki, sa'an nan aka sanya girgijen ya kãma da wuta a kansu suka ƙõne kurmus kamar an gasa fãra. Suka kõma tõka kamar yadda suka nema daga Shu'aibu da a jefa musu ɓaɓɓake daga sama idan ya zama daga mãsu gaskiya.