* Anã ce wa Yahũdãwa 'waɗanda suka tũba,' dõmin sun sãɓã wa maganar Annabinsu,Mũsã, wanda ya ce wa Allah,"Mun tũba zuwa gare Ka." Saba'ãwa su ne mãsu bauta wa malã'iku daga cikin Lãrabãwa ko Yahũdãwa. Nasãra sũ ne waɗanda suka bi Annabi Ĩsa Ɗan Maryamu, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Majũsãwa sũ ne mãsu bautã wa wuta da irin addinin Fãrisa. Mãsu shirki, su ne mãsu bauta wa, gumãka kõ aljannu kõ waɗansu mutãne, wãtau irin addinin Lãrabãwa na lõkacin Jãhiliyya da irin bautar da waɗansu Musulmi ke yi wa waliyyai a yanzu.
* Kuma ya kasa mutãne ƙungiya biyu, ƙungiyar farko sũne mãsu bin addinin gaskiya, ƙungiya ta biyu sũ ne mãsu karkace wa addinin gaskiya, kamar kasũsuwa uku na farko. A kõ da yaushe akwai husũma a tsakãnin ƙungiyoyin biyu. Sa'an nan ya ambaci sakamakon ƙungiyar ƙarya ta farkon,.
* Sakamakon ƙungiya ta gaskiya, wãtau muminai.