पवित्र कुरअानको अर्थको अनुवाद - हौसा अनुवाद : अबू बक्र जोमी

Al'a'ala

external-link copy
1 : 87

سَبِّحِ ٱسۡمَ رَبِّكَ ٱلۡأَعۡلَى

Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 87

ٱلَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ

Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 87

وَٱلَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ

Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri). info
التفاسير:

external-link copy
4 : 87

وَٱلَّذِيٓ أَخۡرَجَ ٱلۡمَرۡعَىٰ

Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 87

فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحۡوَىٰ

Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 87

سَنُقۡرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ

Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 87

إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ وَمَا يَخۡفَىٰ

Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 87

وَنُيَسِّرُكَ لِلۡيُسۡرَىٰ

Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 87

فَذَكِّرۡ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكۡرَىٰ

Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 87

سَيَذَّكَّرُ مَن يَخۡشَىٰ

Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 87

وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلۡأَشۡقَى

Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta, info
التفاسير:

external-link copy
12 : 87

ٱلَّذِي يَصۡلَى ٱلنَّارَ ٱلۡكُبۡرَىٰ

Wanda zai shiga wutar da tã fi girma. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 87

ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ

Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 87

قَدۡ أَفۡلَحَ مَن تَزَكَّىٰ

Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 87

وَذَكَرَ ٱسۡمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ

Kuma ya ambaci sũnan* Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla. info

* Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran.

التفاسير:

external-link copy
16 : 87

بَلۡ تُؤۡثِرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا

Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.* info

* Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira.

التفاسير:

external-link copy
17 : 87

وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰٓ

Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 87

إِنَّ هَٰذَا لَفِي ٱلصُّحُفِ ٱلۡأُولَىٰ

Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko. info

* Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko.

التفاسير:

external-link copy
19 : 87

صُحُفِ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ

Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã. info
التفاسير: