पवित्र कुरअानको अर्थको अनुवाद - हौसा अनुवाद : अबू बक्र जोमी

Al'kamar

external-link copy
1 : 54

ٱقۡتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلۡقَمَرُ

Sã'a ta yi kusa, kuma wata *ya tsãge. info

* Ƙuraishãwa suka nemi Annabi ya yi addu'a dõmin wata ya tsãge wani ɓangaren nãsa ya fãɗo a ƙasã; ya yi addu'ar, watã ya tsãge, wani abu daga gare shi ya fãɗo kamar yadda suka nema.

التفاسير:

external-link copy
2 : 54

وَإِن يَرَوۡاْ ءَايَةٗ يُعۡرِضُواْ وَيَقُولُواْ سِحۡرٞ مُّسۡتَمِرّٞ

Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!" info
التفاسير:

external-link copy
3 : 54

وَكَذَّبُواْ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَكُلُّ أَمۡرٖ مُّسۡتَقِرّٞ

Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 54

وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّنَ ٱلۡأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزۡدَجَرٌ

Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 54

حِكۡمَةُۢ بَٰلِغَةٞۖ فَمَا تُغۡنِ ٱلنُّذُرُ

Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 54

فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡۘ يَوۡمَ يَدۡعُ ٱلدَّاعِ إِلَىٰ شَيۡءٖ نُّكُرٍ

Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 54

خُشَّعًا أَبۡصَٰرُهُمۡ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ كَأَنَّهُمۡ جَرَادٞ مُّنتَشِرٞ

¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 54

مُّهۡطِعِينَ إِلَى ٱلدَّاعِۖ يَقُولُ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَسِرٞ

Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!" info
التفاسير:

external-link copy
9 : 54

۞ كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ فَكَذَّبُواْ عَبۡدَنَا وَقَالُواْ مَجۡنُونٞ وَٱزۡدُجِرَ

Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 54

فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَغۡلُوبٞ فَٱنتَصِرۡ

Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako." info
التفاسير:

external-link copy
11 : 54

فَفَتَحۡنَآ أَبۡوَٰبَ ٱلسَّمَآءِ بِمَآءٖ مُّنۡهَمِرٖ

Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 54

وَفَجَّرۡنَا ٱلۡأَرۡضَ عُيُونٗا فَٱلۡتَقَى ٱلۡمَآءُ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ قَدۡ قُدِرَ

Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 54

وَحَمَلۡنَٰهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلۡوَٰحٖ وَدُسُرٖ

Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 54

تَجۡرِي بِأَعۡيُنِنَا جَزَآءٗ لِّمَن كَانَ كُفِرَ

Tanã gudãna, a kan idãnun Mu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 54

وَلَقَد تَّرَكۡنَٰهَآ ءَايَةٗ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ

Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni info
التفاسير:

external-link copy
16 : 54

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ

To, yãyã azãbã Ta take da gargaɗi Na? info
التفاسير:

external-link copy
17 : 54

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ

Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? info
التفاسير:

external-link copy
18 : 54

كَذَّبَتۡ عَادٞ فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ

Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗi Na? info
التفاسير:

external-link copy
19 : 54

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِي يَوۡمِ نَحۡسٖ مُّسۡتَمِرّٖ

Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 54

تَنزِعُ ٱلنَّاسَ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٖ مُّنقَعِرٖ

Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 54

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ

To, yãya azãbã Ta take da gargaɗi Na? info
التفاسير:

external-link copy
22 : 54

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ

Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? info
التفاسير:

external-link copy
23 : 54

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِٱلنُّذُرِ

Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 54

فَقَالُوٓاْ أَبَشَرٗا مِّنَّا وَٰحِدٗا نَّتَّبِعُهُۥٓ إِنَّآ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٍ

Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 54

أَءُلۡقِيَ ٱلذِّكۡرُ عَلَيۡهِ مِنۢ بَيۡنِنَا بَلۡ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٞ

"Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!" info
التفاسير:

external-link copy
26 : 54

سَيَعۡلَمُونَ غَدٗا مَّنِ ٱلۡكَذَّابُ ٱلۡأَشِرُ

Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan? info
التفاسير:

external-link copy
27 : 54

إِنَّا مُرۡسِلُواْ ٱلنَّاقَةِ فِتۡنَةٗ لَّهُمۡ فَٱرۡتَقِبۡهُمۡ وَٱصۡطَبِرۡ

Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar* ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri. info

* Mutãnen Sãleh sun nemi mu'ujiza da rãƙuma, a fitar da ita daga dũtse, sai aka fitar da ita, kuma aka raba ruwan sha a tsakãninsu da ita.

التفاسير:

external-link copy
28 : 54

وَنَبِّئۡهُمۡ أَنَّ ٱلۡمَآءَ قِسۡمَةُۢ بَيۡنَهُمۡۖ كُلُّ شِرۡبٖ مُّحۡتَضَرٞ

Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 54

فَنَادَوۡاْ صَاحِبَهُمۡ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَ

Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta, info
التفاسير:

external-link copy
30 : 54

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ

To, yãya azãbaTa take da gargaɗi Na? info
التفاسير:

external-link copy
31 : 54

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَكَانُواْ كَهَشِيمِ ٱلۡمُحۡتَظِرِ

Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 54

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? info
التفاسير:

external-link copy
33 : 54

كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطِۭ بِٱلنُّذُرِ

Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 54

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ حَاصِبًا إِلَّآ ءَالَ لُوطٖۖ نَّجَّيۡنَٰهُم بِسَحَرٖ

Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 54

نِّعۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَاۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي مَن شَكَرَ

Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 54

وَلَقَدۡ أَنذَرَهُم بَطۡشَتَنَا فَتَمَارَوۡاْ بِٱلنُّذُرِ

Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 54

وَلَقَدۡ رَٰوَدُوهُ عَن ضَيۡفِهِۦ فَطَمَسۡنَآ أَعۡيُنَهُمۡ فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ

Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩ Na." info
التفاسير:

external-link copy
38 : 54

وَلَقَدۡ صَبَّحَهُم بُكۡرَةً عَذَابٞ مُّسۡتَقِرّٞ

Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 54

فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ

To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩ Na. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 54

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? info
التفاسير:

external-link copy
41 : 54

وَلَقَدۡ جَآءَ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ ٱلنُّذُرُ

Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna. info
التفاسير:

external-link copy
42 : 54

كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذۡنَٰهُمۡ أَخۡذَ عَزِيزٖ مُّقۡتَدِرٍ

Sun ƙaryata game da ãyõyin Mu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi. info
التفاسير:

external-link copy
43 : 54

أَكُفَّارُكُمۡ خَيۡرٞ مِّنۡ أُوْلَٰٓئِكُمۡ أَمۡ لَكُم بَرَآءَةٞ فِي ٱلزُّبُرِ

Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai? info
التفاسير:

external-link copy
44 : 54

أَمۡ يَقُولُونَ نَحۡنُ جَمِيعٞ مُّنتَصِرٞ

Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?" info
التفاسير:

external-link copy
45 : 54

سَيُهۡزَمُ ٱلۡجَمۡعُ وَيُوَلُّونَ ٱلدُّبُرَ

Zã a karya* tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu. info

* Bushãra ce ga Annabi, cewa zai yi yãƙi da Kuraishi kuma zai rinjãye su. Sa'an nan yãkin ya auku a Badar.

التفاسير:

external-link copy
46 : 54

بَلِ ٱلسَّاعَةُ مَوۡعِدُهُمۡ وَٱلسَّاعَةُ أَدۡهَىٰ وَأَمَرُّ

Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci. info
التفاسير:

external-link copy
47 : 54

إِنَّ ٱلۡمُجۡرِمِينَ فِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٖ

Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka. info
التفاسير:

external-link copy
48 : 54

يَوۡمَ يُسۡحَبُونَ فِي ٱلنَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ ذُوقُواْ مَسَّ سَقَرَ

Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar." info
التفاسير:

external-link copy
49 : 54

إِنَّا كُلَّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَٰهُ بِقَدَرٖ

Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri. info
التفاسير:

external-link copy
50 : 54

وَمَآ أَمۡرُنَآ إِلَّا وَٰحِدَةٞ كَلَمۡحِۭ بِٱلۡبَصَرِ

Kuma umurnin Mu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido. info
التفاسير:

external-link copy
51 : 54

وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَآ أَشۡيَاعَكُمۡ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ

Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni? info
التفاسير:

external-link copy
52 : 54

وَكُلُّ شَيۡءٖ فَعَلُوهُ فِي ٱلزُّبُرِ

Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai. info
التفاسير:

external-link copy
53 : 54

وَكُلُّ صَغِيرٖ وَكَبِيرٖ مُّسۡتَطَرٌ

Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne. info
التفاسير:

external-link copy
54 : 54

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّٰتٖ وَنَهَرٖ

Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna. info
التفاسير:

external-link copy
55 : 54

فِي مَقۡعَدِ صِدۡقٍ عِندَ مَلِيكٖ مُّقۡتَدِرِۭ

A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa. info
التفاسير: