पवित्र कुरअानको अर्थको अनुवाद - हौसा अनुवाद : अबू बक्र जोमी

رقم الصفحة:close

external-link copy
109 : 11

فَلَا تَكُ فِي مِرۡيَةٖ مِّمَّا يَعۡبُدُ هَٰٓؤُلَآءِۚ مَا يَعۡبُدُونَ إِلَّا كَمَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُهُم مِّن قَبۡلُۚ وَإِنَّا لَمُوَفُّوهُمۡ نَصِيبَهُمۡ غَيۡرَ مَنقُوصٖ

Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba. info
التفاسير:

external-link copy
110 : 11

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَٱخۡتُلِفَ فِيهِۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ

Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã* wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto. info

* Yahũdãwa sun sãɓa wa jũna a cikin littattafan da aka bai wa Mũsã. To, ku Musulmi kada ku bi hanyarsu, har ku sãɓawa Allah, har abin da ya sãme su ya sãme ku.

التفاسير:

external-link copy
111 : 11

وَإِنَّ كُلّٗا لَّمَّا لَيُوَفِّيَنَّهُمۡ رَبُّكَ أَعۡمَٰلَهُمۡۚ إِنَّهُۥ بِمَا يَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Kuma lalle, haƙĩƙa, Ubangijinka Mai cika wa kõwa (sakamakon) Ayyukan sa ne. Lalle Shĩ, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke aikatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
112 : 11

فَٱسۡتَقِمۡ كَمَآ أُمِرۡتَ وَمَن تَابَ مَعَكَ وَلَا تَطۡغَوۡاْۚ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Sai ka daidaitu* kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. info

* Wannan ãyã tanã hana dukan bidi'a a cikin addini. Tun da ba a yarda Annabi ya ƙara ra'ayinsa ba sai dai ya bi umurnin Allah kamar yadda Ya yi umurnin, kuma haka ne Ya umurci wanda ya bi Annabi. Sabõda haka mai sãɓa wa umurnin Allah da ƙãri ko ragi, bã ya cikin mabiyan Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

التفاسير:

external-link copy
113 : 11

وَلَا تَرۡكَنُوٓاْ إِلَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ فَتَمَسَّكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِنۡ أَوۡلِيَآءَ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ

Kada ku karkata* zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba. info

* Ba ya halatta ga Musulmi ya karkata zuwa ga kãfirai kamar yadda bã ya halatta ya karkata a cikin addininsa. Wannan shĩ ne babban makãmi a kan mãƙĩya.

التفاسير:

external-link copy
114 : 11

وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّٰكِرِينَ

Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. Wancan* ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa. info

* Tsayar da sallõli farillai tãre da Lĩman a cikin masallatai shĩ ne zikiri ga mai son zikirin gaskiya. Ayyukan ƙwarai sunã shãfe miyãgu.

التفاسير:

external-link copy
115 : 11

وَٱصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa.* info

* Haƙuri a kan ibãda wãjibi ne, haka kuma kyautatãwa, wãtau shĩ ne yin kõwãne aiki na ibãda tsantsa kamar salla kõ na ma'amala kamar ciniki da aure, dõmĩn Allah kawai. An yi wa wannan fanni na biyu sũna da "Tasawwuf", bidi'a ne dõmin bai taho daga sunna ba. Asalinsa "theosophy" daga lugar Ajam, ma'anarsa neman hikima ta Allah a hãlin keɓance kai a cikin kaɗaita da wasu aikace-aikace na ibada, kamar girka ga 'yanbõri.

التفاسير:

external-link copy
116 : 11

فَلَوۡلَا كَانَ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مِن قَبۡلِكُمۡ أُوْلُواْ بَقِيَّةٖ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡفَسَادِ فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّنۡ أَنجَيۡنَا مِنۡهُمۡۗ وَٱتَّبَعَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَآ أُتۡرِفُواْ فِيهِ وَكَانُواْ مُجۡرِمِينَ

To, don me mãsu hankali ba su kasance daga mutãnen ƙarnõnin da suke a gabãninku ba, sunã hani daga ɓarna a cikin ƙasa? fãce kaɗan daga wanda Muka kuɓutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma waɗanda suka yi zãlunci suka bin abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance mãsu laifi. info
التفاسير:

external-link copy
117 : 11

وَمَا كَانَ رَبُّكَ لِيُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ بِظُلۡمٖ وَأَهۡلُهَا مُصۡلِحُونَ

Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alƙaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa.* info

* Wannan ãyã da ta sama da ita sunã nũna muhimmancin wa'azi a cikin kõwane hãli na al'umma, dõmin tsarewar zamanta al'umma.

التفاسير: