* Tafarkin Allah, (fi sabilillahi)a wannan sũra tanã nufin jihãdi na takõbi dõmin ɗaukaka kalmar Allah da tsare ta. Anã fassara tafarkin Allah a waɗansu wurãre da jihãdi na takõbi kõ na magana dõmin shiryar da mutãne kõ dõmin tsaron gaskiya, kõ kuma karantarwa, da kuma tsare rai daga sha'awarta da fushinta. A cikin Hadisi anã ruwaitõwa cewa tsaron rai daga sha'awarta da fushinta shĩ ne jihãdi wanda ya fi girma.
* Tabbatar da dugadugan ƙafãfun, yanã nufin sanya musu jãrumta a cikin zukãtansu, dõmin ƙafãfunsu, su kafu a wurin yaƙi, dõmin kada su gudu.