* Ku tunkuɗe mana maƙiyã da duhunku, kõ dã ba ku yi yãƙi ba.
* A cikin Hadisi an ruwaito cewa, Annabi yã ce Allah Yanã sanya rũhinsu a cikin cikkunan tsuntsãye mãsu kõren launi, sunã tafiya da su a cikin Aljanna sunã ci daga 'ya'yan itãcenta da rãna, sa'an nan su kõma zuwa ga wasu fitillu waɗanda aka rãtaye a cikin inuwar Al'arshi.
* Bayan kõmawar Musulmi daga Uhdu da miyãkun da suka sãme su, sai Annabi ya umurce su da fita a bãyan kãfirai, dõmin kada su yi tunãnin kõmãwa. Sai suka fita bãyansu, aka dãce kuwa Abu Sufyãna ya umurci mutãnensa da kõmawa Madĩna dõmin su tumɓuke Musulmi. An yi Uhdu ta farko ran Asabat, sa'an nan suka fita a bãyansu a rãnar Lahadi, suka riske su a Hamra'al Asad. Sai aka yi tawãfuƙi (yarjejeniya) tsakanin Annabi da Abu Sufyãna a kan a bar yãƙi a lõkacin, sai shekara mai zuwa, a haɗu a Badar. Allah Ya yabi Musulmi, da suka karɓa wannan kira, a cikin miyãkũ. Haka duka mai karɓawa irinsu, yã shiga a cikin irin wannan yabo har ya zuwa tãshin Ƙiyãma. ** Kyautata yi shi ne tsarkake aiki dõmin Allah watau ihsani kõ ihlasi.
* Yãƙin Badar na Uku, a cikin shekara ta huɗu yake, a watan Sha'aban. Badar kãsuwa ce babba ga ƙabĩlun Lãrabãwa a kõwace shekara. A bãyan Uhdu an yi alkawari da Abu Sufyãna, a kan a haɗu a Badr shekara mai zuwa. Sabõda haka sai Abu Sufyãna ya fita daga Makka har ya sauka Marriz zahrãn, sai Allah Ya sanya masa tsõro a cikin zũciyarsa sai ya gamu da Nu'aima bn Mas'ũd el Ashja'iy, ya ce masa: "Ni nã yi alkawari da Muhammadu a kan mu haɗu a Kãsuwar Badar. Wannan kuwa shekar fari ce. Inã son sãɓãwar alkawarin ta zama daga gare shi, bã daga gare ni ba. Ka tafi Madĩna ka yi ƙõƙarin hana su fitõwa, zan bã ka rãƙuma gõma." Sai Nu'aimu ya tafi Madĩna ya iske Annabi da Sahabbansa suna shirin fita. Sai ya ce musu: "Me kuke nufi?" Suka ce; " Alkawarin Abu Sufyãna." Sai ya ce: "Bã zã ku iya ba, dõmin kuwa sun tãra rundunõni sabõda ku." Sai Annabi ya ce: "Zan fita kõ da nĩ kaɗai ne." Sai Annabi ya fita da mutum dubu da ɗari biyar, suka tafi Badar bãbu Abu Sufyãna. Suka ci kãsuwa suka kõmo.