ಪವಿತ್ರ ಕುರ್‌ಆನ್ ಅರ್ಥಾನುವಾದ - ಹೌಸಾ ಅನುವಾದ - ಅಬೂಬಕರ್ ಜೋಮಿ

Al'ifidar

external-link copy
1 : 82

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتۡ

Idan sama ta tsãge. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 82

وَإِذَا ٱلۡكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتۡ

Kuma idan taurãri suka wãtse. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 82

وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ فُجِّرَتۡ

Kuma idan tẽkuna aka facce su. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 82

وَإِذَا ٱلۡقُبُورُ بُعۡثِرَتۡ

Kuma idan kaburbura aka tõne su. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 82

عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ وَأَخَّرَتۡ

Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 82

يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلۡكَرِيمِ

Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 82

ٱلَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ

Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 82

فِيٓ أَيِّ صُورَةٖ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ

A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 82

كَلَّا بَلۡ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ

A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako! info
التفاسير:

external-link copy
10 : 82

وَإِنَّ عَلَيۡكُمۡ لَحَٰفِظِينَ

Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 82

كِرَامٗا كَٰتِبِينَ

Mãsu daraja, marubũta. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 82

يَعۡلَمُونَ مَا تَفۡعَلُونَ

Sunã sanin abin da kuke aikatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 82

إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٖ

Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 82

وَإِنَّ ٱلۡفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٖ

Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 82

يَصۡلَوۡنَهَا يَوۡمَ ٱلدِّينِ

Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 82

وَمَا هُمۡ عَنۡهَا بِغَآئِبِينَ

Bã zã su faku daga gare ta ba. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 82

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako? info
التفاسير:

external-link copy
18 : 82

ثُمَّ مَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ

Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako? info
التفاسير:

external-link copy
19 : 82

يَوۡمَ لَا تَمۡلِكُ نَفۡسٞ لِّنَفۡسٖ شَيۡـٔٗاۖ وَٱلۡأَمۡرُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ

Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake. info
التفاسير: