ಪವಿತ್ರ ಕುರ್‌ಆನ್ ಅರ್ಥಾನುವಾದ - ಹೌಸಾ ಅನುವಾದ - ಅಬೂಬಕರ್ ಜೋಮಿ

ಪುಟ ಸಂಖ್ಯೆ:close

external-link copy
17 : 40

ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۚ لَا ظُلۡمَ ٱلۡيَوۡمَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Yau anã sãka wa kõwane rai a game da abin da ya aikata, bãbu zãlunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisãbi ne. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 40

وَأَنذِرۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡأٓزِفَةِ إِذِ ٱلۡقُلُوبُ لَدَى ٱلۡحَنَاجِرِ كَٰظِمِينَۚ مَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ حَمِيمٖ وَلَا شَفِيعٖ يُطَاعُ

Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar (Sã'a) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu). info
التفاسير:

external-link copy
19 : 40

يَعۡلَمُ خَآئِنَةَ ٱلۡأَعۡيُنِ وَمَا تُخۡفِي ٱلصُّدُورُ

(Allah) Ya san yaudarar idãnu da abin da ƙirãza ke ɓõyẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 40

وَٱللَّهُ يَقۡضِي بِٱلۡحَقِّۖ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَقۡضُونَ بِشَيۡءٍۗ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Kuma Allah Shĩ ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, wanin Sa, bã su yin hukunci da kõme. Lalle Allah, Shĩ ne Mai ji, Mai gani. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 40

۞ أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ كَانُواْ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُواْ هُمۡ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡ وَمَا كَانَ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ

Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu. Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 40

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانَت تَّأۡتِيهِمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَكَفَرُواْ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ قَوِيّٞ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azãba. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 40

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã a game da ãyõyinMu da wani dalĩli bayyananne. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 40

إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَ وَقَٰرُونَ فَقَالُواْ سَٰحِرٞ كَذَّابٞ

Zuwa ga Fir'auna da Hãmãna da Kãrũna, sai suka ce: "Mai sihiri ne, maƙaryaci." info
التفاسير:

external-link copy
25 : 40

فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلۡحَقِّ مِنۡ عِندِنَا قَالُواْ ٱقۡتُلُوٓاْ أَبۡنَآءَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ وَٱسۡتَحۡيُواْ نِسَآءَهُمۡۚ وَمَا كَيۡدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ

Sa'an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: "Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu." Kuma mugun shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata. info
التفاسير: