ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី

Al'dhuha

external-link copy
1 : 93

وَٱلضُّحَىٰ

Inã rantsuwa da hantsi. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 93

وَٱلَّيۡلِ إِذَا سَجَىٰ

Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa). info
التفاسير:

external-link copy
3 : 93

مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ

Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 93

وَلَلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ

Kuma lalle ta ƙarshe* ce mafi alheri a gare ka daga ta farko. info

* Ta ƙarshe, wãto, Lãhira; kuma ta farko, wato, dũniya.

التفاسير:

external-link copy
5 : 93

وَلَسَوۡفَ يُعۡطِيكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰٓ

Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 93

أَلَمۡ يَجِدۡكَ يَتِيمٗا فَـَٔاوَىٰ

Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma? info
التفاسير:

external-link copy
7 : 93

وَوَجَدَكَ ضَآلّٗا فَهَدَىٰ

Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai? info
التفاسير:

external-link copy
8 : 93

وَوَجَدَكَ عَآئِلٗا فَأَغۡنَىٰ

Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka? info
التفاسير:

external-link copy
9 : 93

فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ

Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 93

وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنۡهَرۡ

Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 93

وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ

Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya). info
التفاسير: