ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី

Al'a'ala

external-link copy
1 : 87

سَبِّحِ ٱسۡمَ رَبِّكَ ٱلۡأَعۡلَى

Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 87

ٱلَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ

Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 87

وَٱلَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ

Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri). info
التفاسير:

external-link copy
4 : 87

وَٱلَّذِيٓ أَخۡرَجَ ٱلۡمَرۡعَىٰ

Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 87

فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحۡوَىٰ

Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 87

سَنُقۡرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ

Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 87

إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ وَمَا يَخۡفَىٰ

Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 87

وَنُيَسِّرُكَ لِلۡيُسۡرَىٰ

Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 87

فَذَكِّرۡ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكۡرَىٰ

Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 87

سَيَذَّكَّرُ مَن يَخۡشَىٰ

Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna. info
التفاسير: