ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី

Nouh

external-link copy
1 : 71

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرۡ قَوۡمَكَ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 71

قَالَ يَٰقَوۡمِ إِنِّي لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٌ

Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa." info
التفاسير:

external-link copy
3 : 71

أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُ وَأَطِيعُونِ

"Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõron Sa, kuma ku bĩ ni." info
التفاسير:

external-link copy
4 : 71

يَغۡفِرۡ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمۡ وَيُؤَخِّرۡكُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمًّىۚ إِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ إِذَا جَآءَ لَا يُؤَخَّرُۚ لَوۡ كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

"Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)." info
التفاسير:

external-link copy
5 : 71

قَالَ رَبِّ إِنِّي دَعَوۡتُ قَوۡمِي لَيۡلٗا وَنَهَارٗا

Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini." info
التفاسير:

external-link copy
6 : 71

فَلَمۡ يَزِدۡهُمۡ دُعَآءِيٓ إِلَّا فِرَارٗا

"To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)." info
التفاسير:

external-link copy
7 : 71

وَإِنِّي كُلَّمَا دَعَوۡتُهُمۡ لِتَغۡفِرَ لَهُمۡ جَعَلُوٓاْ أَصَٰبِعَهُمۡ فِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَٱسۡتَغۡشَوۡاْ ثِيَابَهُمۡ وَأَصَرُّواْ وَٱسۡتَكۡبَرُواْ ٱسۡتِكۡبَارٗا

"Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai." info
التفاسير:

external-link copy
8 : 71

ثُمَّ إِنِّي دَعَوۡتُهُمۡ جِهَارٗا

"Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane." info
التفاسير:

external-link copy
9 : 71

ثُمَّ إِنِّيٓ أَعۡلَنتُ لَهُمۡ وَأَسۡرَرۡتُ لَهُمۡ إِسۡرَارٗا

"Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri." info
التفاسير:

external-link copy
10 : 71

فَقُلۡتُ ٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ إِنَّهُۥ كَانَ غَفَّارٗا

"Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne." info
التفاسير: