ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី

លេខ​ទំព័រ:close

external-link copy
17 : 59

فَكَانَ عَٰقِبَتَهُمَآ أَنَّهُمَا فِي ٱلنَّارِ خَٰلِدَيۡنِ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَٰٓؤُاْ ٱلظَّٰلِمِينَ

Sai ãƙibarsu ta kasance cẽwa su biyun duka sunã a cikin wutã, sunã mãsu dawwama a cikinta. "Kuma wannan shĩ ne sakamakon mãsu zãlunci." info
التفاسير:

external-link copy
18 : 59

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلۡتَنظُرۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ لِغَدٖۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa.* info

* Daga wannan ãyã ta l8 zuwa ƙarshen sũra, yanã bayãnin hãsalin darasin sũrar ne dunƙule, da kuma ambatar muhimman abũbuwan da ta ƙunsa dõmin wa'azi da farkarwa ga mai hankali.

التفاسير:

external-link copy
19 : 59

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ نَسُواْ ٱللَّهَ فَأَنسَىٰهُمۡ أَنفُسَهُمۡۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rãyu, kansu. Waɗannan sũ ne fãsiƙai. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 59

لَا يَسۡتَوِيٓ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۚ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ

Yan Wutã da 'yan Aljanna bã su daidaita. 'Yan Aljanna, sũ ne mãsu babban rabo. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 59

لَوۡ أَنزَلۡنَا هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ عَلَىٰ جَبَلٖ لَّرَأَيۡتَهُۥ خَٰشِعٗا مُّتَصَدِّعٗا مِّنۡ خَشۡيَةِ ٱللَّهِۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَمۡثَٰلُ نَضۡرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

Dã Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dũtse, dã lalle kã ga dũtsen yanã mai tawãli'u, mai tsattsãgẽwa sabõda tsõron Allah, kuma waɗancan misãlai Munã bayyana su ne ga mutãne, da fatan za su yi tunãni. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 59

هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۖ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ

(Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 59

هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡقُدُّوسُ ٱلسَّلَٰمُ ٱلۡمُؤۡمِنُ ٱلۡمُهَيۡمِنُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡجَبَّارُ ٱلۡمُتَكَبِّرُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Shĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai tastãwa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 59

هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡخَٰلِقُ ٱلۡبَارِئُ ٱلۡمُصَوِّرُۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Shĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa. Yanã da sũnãye mãsu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. info
التفاسير: