ការបកប្រែអត្ថន័យគួរអាន - ការបកប្រែជាភាសាhausa- អាពូពេីកេីរ​ ជូមុី

លេខ​ទំព័រ:close

external-link copy
38 : 11

وَيَصۡنَعُ ٱلۡفُلۡكَ وَكُلَّمَا مَرَّ عَلَيۡهِ مَلَأٞ مِّن قَوۡمِهِۦ سَخِرُواْ مِنۡهُۚ قَالَ إِن تَسۡخَرُواْ مِنَّا فَإِنَّا نَسۡخَرُ مِنكُمۡ كَمَا تَسۡخَرُونَ

Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnen sa suka shũɗe a gaban sa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 11

فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ مَن يَأۡتِيهِ عَذَابٞ يُخۡزِيهِ وَيَحِلُّ عَلَيۡهِ عَذَابٞ مُّقِيمٌ

"Sa'an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira)." info
التفاسير:

external-link copy
40 : 11

حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَمۡرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ قُلۡنَا ٱحۡمِلۡ فِيهَا مِن كُلّٖ زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَأَهۡلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيۡهِ ٱلۡقَوۡلُ وَمَنۡ ءَامَنَۚ وَمَآ ءَامَنَ مَعَهُۥٓ إِلَّا قَلِيلٞ

Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa*, da wanda ya yi ĩmãni." Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan." info

* Iyalan Nũhu sun yi ĩmãni banda ɗansa Yãmu, da matarsa guda kãfira. Waɗanda suka yi ĩmãni daga sauran mutãnensa tamãnin ne maza da mãtã. Amma kuma an ce mutãne saba'in da biyu ne, kuma an ce gõma ne. Allah ne Mafi sani.

التفاسير:

external-link copy
41 : 11

۞ وَقَالَ ٱرۡكَبُواْ فِيهَا بِسۡمِ ٱللَّهِ مَجۡر۪ىٰهَا وَمُرۡسَىٰهَآۚ إِنَّ رَبِّي لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ

Kuma ya ce: "Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudãnarta da matabbatarta. Lalle ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." info
التفاسير:

external-link copy
42 : 11

وَهِيَ تَجۡرِي بِهِمۡ فِي مَوۡجٖ كَٱلۡجِبَالِ وَنَادَىٰ نُوحٌ ٱبۡنَهُۥ وَكَانَ فِي مَعۡزِلٖ يَٰبُنَيَّ ٱرۡكَب مَّعَنَا وَلَا تَكُن مَّعَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma ita tanã gudãna da su a cikin tãguwar ruwa kamai duwãtsu, sai Nũhu ya kirãyi ɗansa alhãli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. "Yã ƙaramin ɗãnã! zo ka hau tãre da mu, kuma kada ka kasance tãre da kãfirai!" info
التفاسير:

external-link copy
43 : 11

قَالَ سَـَٔاوِيٓ إِلَىٰ جَبَلٖ يَعۡصِمُنِي مِنَ ٱلۡمَآءِۚ قَالَ لَا عَاصِمَ ٱلۡيَوۡمَ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِ إِلَّا مَن رَّحِمَۚ وَحَالَ بَيۡنَهُمَا ٱلۡمَوۡجُ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُغۡرَقِينَ

Ya ce: "Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan." (Nũhu) ya ce: "Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama." Sai taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãnin su, sai ya kasance daga waɗan da aka nutsar. info
التفاسير:

external-link copy
44 : 11

وَقِيلَ يَٰٓأَرۡضُ ٱبۡلَعِي مَآءَكِ وَيَٰسَمَآءُ أَقۡلِعِي وَغِيضَ ٱلۡمَآءُ وَقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ وَٱسۡتَوَتۡ عَلَى ٱلۡجُودِيِّۖ وَقِيلَ بُعۡدٗا لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ

Kuma aka ce: "Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme."Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi*, kuma aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutãne Azzãlumai." info

* Judiyyu sũnan wani dũtse ne a cikin Jazĩra. Jirgin Nũhu ya zauna a kansa, har mutãnen farko na wannan al'umma sun gan shi. Sa'an nan ya halaka.

التفاسير:

external-link copy
45 : 11

وَنَادَىٰ نُوحٞ رَّبَّهُۥ فَقَالَ رَبِّ إِنَّ ٱبۡنِي مِنۡ أَهۡلِي وَإِنَّ وَعۡدَكَ ٱلۡحَقُّ وَأَنتَ أَحۡكَمُ ٱلۡحَٰكِمِينَ

Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu yin hukunci." info
التفاسير: