Terjemahan makna Alquran Alkarim - Terjemahan Berbahasa Hausa - Abu Bakar Jomy

Al'fajr

external-link copy
1 : 89

وَٱلۡفَجۡرِ

Inã rantsuwa da alfijiri. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 89

وَلَيَالٍ عَشۡرٖ

Da darũruwa gõma. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 89

وَٱلشَّفۡعِ وَٱلۡوَتۡرِ

Da (adadi na) cikã da (na) mãrã. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 89

وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَسۡرِ

Da dare idan yana shũɗewa. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 89

هَلۡ فِي ذَٰلِكَ قَسَمٞ لِّذِي حِجۡرٍ

Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)? info
التفاسير:

external-link copy
6 : 89

أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ

Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba? info
التفاسير:

external-link copy
7 : 89

إِرَمَ ذَاتِ ٱلۡعِمَادِ

Iramawa mãsu sakon* ƙĩrar jiki. info

* Tsawo mai ma'ana.

التفاسير:

external-link copy
8 : 89

ٱلَّتِي لَمۡ يُخۡلَقۡ مِثۡلُهَا فِي ٱلۡبِلَٰدِ

Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya). info
التفاسير:

external-link copy
9 : 89

وَثَمُودَ ٱلَّذِينَ جَابُواْ ٱلصَّخۡرَ بِٱلۡوَادِ

Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi* suka yi gidãje)? info

* Wãdil-ƙura, sunan wuri ne kusa da Madina wajen Syria, wato Sham.

التفاسير:

external-link copy
10 : 89

وَفِرۡعَوۡنَ ذِي ٱلۡأَوۡتَادِ

Da Fir'auna mai turãku. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 89

ٱلَّذِينَ طَغَوۡاْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ

Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa? info
التفاسير:

external-link copy
12 : 89

فَأَكۡثَرُواْ فِيهَا ٱلۡفَسَادَ

Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 89

فَصَبَّ عَلَيۡهِمۡ رَبُّكَ سَوۡطَ عَذَابٍ

Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 89

إِنَّ رَبَّكَ لَبِٱلۡمِرۡصَادِ

Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 89

فَأَمَّا ٱلۡإِنسَٰنُ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكۡرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَكۡرَمَنِ

To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni." info
التفاسير:

external-link copy
16 : 89

وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيۡهِ رِزۡقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَهَٰنَنِ

Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni." info
التفاسير:

external-link copy
17 : 89

كَلَّاۖ بَل لَّا تُكۡرِمُونَ ٱلۡيَتِيمَ

A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya! info
التفاسير:

external-link copy
18 : 89

وَلَا تَحَٰٓضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ

Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci! info
التفاسير:

external-link copy
19 : 89

وَتَأۡكُلُونَ ٱلتُّرَاثَ أَكۡلٗا لَّمّٗا

Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 89

وَتُحِبُّونَ ٱلۡمَالَ حُبّٗا جَمّٗا

Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 89

كَلَّآۖ إِذَا دُكَّتِ ٱلۡأَرۡضُ دَكّٗا دَكّٗا

A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 89

وَجَآءَ رَبُّكَ وَٱلۡمَلَكُ صَفّٗا صَفّٗا

Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu. info
التفاسير: