* Allah nã zaɓen Manzanni daga mutãne da malã'iku kawai. Sabõ da haka bãbu wani manzo da jinsin aljannu kõ wani jinsi, kuma ãyar Sũratul Ahzãb ta 40 tã nũna zãɓen nan ya ƙãre daga Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Duk wanda ya yi da'awar Allah Ya bã shi wani hukumci a bãyan Annabi Muhammadu, kõ dã bai yi da'awar annabci ba, to, shĩ Dajjal ne, bã a bin sa.
* Bãbu ƙunci a cikin Musulunci, duk inda aka faɗi tsanani kuma an faɗi yadda sauƙi zai sãmu a kõwane hãli. ** Sharaɗin Musulunci ya zama a kan aƙĩdar Ibrãhĩm wanda ya yi wa wannan al'umma sũna da Musulmi tun a zãmaninsa, kuma an ambaci wannan magana a cikin wannan Littafi, wãtau Alƙur'ãni, a cikin sũrar Baƙara ãyã ta 128.