કુરઆન મજીદના શબ્દોનું ભાષાંતર - હૌસા ભાષામાં અનુવાદ - અબૂ બકર જૂમી

Al'teen

external-link copy
1 : 95

وَٱلتِّينِ وَٱلزَّيۡتُونِ

Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.* info

* Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'.

التفاسير:

external-link copy
2 : 95

وَطُورِ سِينِينَ

Da Dũr Sĩnĩna.* info

* Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa.

التفاسير:

external-link copy
3 : 95

وَهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٱلۡأَمِينِ

Da wannan gari* amintacce. info

* Gari amintacce shi ne Makkah.

التفاسير:

external-link copy
4 : 95

لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِيٓ أَحۡسَنِ تَقۡوِيمٖ

Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 95

ثُمَّ رَدَدۡنَٰهُ أَسۡفَلَ سَٰفِلِينَ

Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni info
التفاسير:

external-link copy
6 : 95

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونٖ

Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 95

فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعۡدُ بِٱلدِّينِ

To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)? info
التفاسير:

external-link copy
8 : 95

أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَحۡكَمِ ٱلۡحَٰكِمِينَ

Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?* info

* Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci.

التفاسير: