કુરઆન મજીદના શબ્દોનું ભાષાંતર - હૌસા ભાષામાં અનુવાદ - અબૂ બકર જૂમી

પેજ નંબર: 286:282 close

external-link copy
50 : 17

۞ قُلۡ كُونُواْ حِجَارَةً أَوۡ حَدِيدًا

Ka ce: "Ku kasance duwãtsu ko kuwa baƙin ƙarfe." info
التفاسير:

external-link copy
51 : 17

أَوۡ خَلۡقٗا مِّمَّا يَكۡبُرُ فِي صُدُورِكُمۡۚ فَسَيَقُولُونَ مَن يُعِيدُنَاۖ قُلِ ٱلَّذِي فَطَرَكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖۚ فَسَيُنۡغِضُونَ إِلَيۡكَ رُءُوسَهُمۡ وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هُوَۖ قُلۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَرِيبٗا

"Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku." To zã su ce "Wãne ne zai mayar da mu?" Ka ce: "Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci." To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, "A yaushene shi?" Ka ce: "Akwai tsammãninsa ya kasance kusa." info
التفاسير:

external-link copy
52 : 17

يَوۡمَ يَدۡعُوكُمۡ فَتَسۡتَجِيبُونَ بِحَمۡدِهِۦ وَتَظُنُّونَ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا

"A rãnar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓãwa game dã gõde Masa, kuma kunã zaton ba ku zauna ba fãce kaɗan." info
التفاسير:

external-link copy
53 : 17

وَقُل لِّعِبَادِي يَقُولُواْ ٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ يَنزَغُ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ كَانَ لِلۡإِنسَٰنِ عَدُوّٗا مُّبِينٗا

Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma* wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyanan ne. info

* Ka ce wa bãyĩNa, mutãne, idan sunã magana su auna kalmõmin da suke zance da su, sa'an nan su riƙa amfãni da kalma mafi kyãwo dõmin kada shaiɗan ya sãmi mashiga daga maganarsu zuwa ga zukãtansu, ya sanya ɓarna a tsakãninsu.

التفاسير:

external-link copy
54 : 17

رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِكُمۡۖ إِن يَشَأۡ يَرۡحَمۡكُمۡ أَوۡ إِن يَشَأۡ يُعَذِّبۡكُمۡۚ وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ وَكِيلٗا

Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kõ kuwa idan Yã so zai azabtãku. Kuma ba Mu aika ka kanã wakĩli a kansu ba. info
التفاسير:

external-link copy
55 : 17

وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِمَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ فَضَّلۡنَا بَعۡضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعۡضٖۖ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.* info

* Muƙãrana a tsakãnin Annabãwa. Allah Yã fĩfĩta waɗansu a kan waɗansu. Falalar Dãwũda a kan waɗansu Annabãwa da Zabũra ne to inã fĩfĩkon wanda aka bai wa Alƙur'ãni mafĩfĩcin littafi da sauran Annabãwa?.

التفاسير:

external-link copy
56 : 17

قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِهِۦ فَلَا يَمۡلِكُونَ كَشۡفَ ٱلضُّرِّ عَنكُمۡ وَلَا تَحۡوِيلًا

Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya, baicinSa." To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa."* info

* Bã zã su iya jũyar da cũta daga gare ku zuwa ga wani ko kuwa daga wani zuwa gare ku ba.

التفاسير:

external-link copy
57 : 17

أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ يَبۡتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلۡوَسِيلَةَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ وَيَرۡجُونَ رَحۡمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحۡذُورٗا

Waɗancan, waɗanda suke kiran*, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce. info

* Waɗanda kãfirai ke neman tawassuli da su zuwa ga Allah, sũ ma sunã neman abin da zai sãdar da su zuwa ga Allah, sabõda haka bãbu bambanci a tsakãnin mai tawassuli da wanda ake tawassulin da shi ga kusanta zuwa ga Allah. Bãbu mai kusanta zuwa ga Allah sai da taƙawa ga ibãdarSa kawai.

التفاسير:

external-link copy
58 : 17

وَإِن مِّن قَرۡيَةٍ إِلَّا نَحۡنُ مُهۡلِكُوهَا قَبۡلَ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَوۡ مُعَذِّبُوهَا عَذَابٗا شَدِيدٗاۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَسۡطُورٗا

Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar ¡iyãma kõ kuwa Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi rubũtacce. info
التفاسير: