Firo maanaaji al-quraan tedduɗo oo - Eggo (nantino) ngoo e Hawsaare - Abubakar Gummi

external-link copy
33 : 34

وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ لِلَّذِينَ ٱسۡتَكۡبَرُواْ بَلۡ مَكۡرُ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ إِذۡ تَأۡمُرُونَنَآ أَن نَّكۡفُرَ بِٱللَّهِ وَنَجۡعَلَ لَهُۥٓ أَندَادٗاۚ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ وَجَعَلۡنَا ٱلۡأَغۡلَٰلَ فِيٓ أَعۡنَاقِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۖ هَلۡ يُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Kuma maraunana suka ce wa makangara. "Ã'a, (ku tuna) mãkircin dare da na rãna a lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan tãrayya." Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa. info
التفاسير: