ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمهه‌ى هوساوى - ابوبكر جومى

Al'dalaq

external-link copy
1 : 65

يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحۡصُواْ ٱلۡعِدَّةَۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ رَبَّكُمۡۖ لَا تُخۡرِجُوهُنَّ مِنۢ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخۡرُجۡنَ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ لَا تَدۡرِي لَعَلَّ ٱللَّهَ يُحۡدِثُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ أَمۡرٗا

Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu,* kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bãyan haka. info

* Saki, shĩ ne warware ƙullin halaccin sãduwa da jũna a tsakãnin miji da mãta. Haƙƙi ne wanda Allah Ya saka ga hannayen maza ban da mãtã. saki ga idda, watau ya sake ta saki gudã a cikin tsarkin dabai shãfe ta ba dõmin sauƙin idda. Yanã haramta ga mijin da mãtar ya fitar da ita kõ ta fita daga ɗãkinta a lõkacin idda. fãruwar wani al'amari shi ne sõyayya a bãyan ƙiyayya da mayarwa a bãyan saki. Alfãsha a nan, tanã nufin faɗa da zãge-zãge a kan surukantã. Anã fitar da mai iddar saki sabõda alfãsha daga gidanta.Akwai saki na sunna kuma akwai na bidi'a, amma saki na sunna ɗaya ne, a cikin tsarkin da bã a shãfe ta ba kuma kada a ƙãra mata wani saki har ta ƙãre idda, sakin bidi'a kuwa shĩne uku gabã ɗaya kõ a cikin idda gudã, a cikin haila kõ jinin bĩƙi. Sakin bidi'a yanã 1azimta, Anã tĩlastã shi mayarwa ga wadda aka saki a cikin haila idan bai kai uku ba ga miji 'yantacce, kõ biyu ga miji bãwã.

التفاسير:

external-link copy
2 : 65

فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ فَارِقُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖ وَأَشۡهِدُواْ ذَوَيۡ عَدۡلٖ مِّنكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَ لِلَّهِۚ ذَٰلِكُمۡ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مَخۡرَجٗا

Sa'an nan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku riƙe su da abin da aka sani kõ ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da mãsu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar dõmin Allah. Wancan ɗinku anã yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yanã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 65

وَيَرۡزُقۡهُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَحۡتَسِبُۚ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَهُوَ حَسۡبُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَٰلِغُ أَمۡرِهِۦۚ قَدۡ جَعَلَ ٱللَّهُ لِكُلِّ شَيۡءٖ قَدۡرٗا

Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 65

وَٱلَّٰٓـِٔي يَئِسۡنَ مِنَ ٱلۡمَحِيضِ مِن نِّسَآئِكُمۡ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَٰثَةُ أَشۡهُرٖ وَٱلَّٰٓـِٔي لَمۡ يَحِضۡنَۚ وَأُوْلَٰتُ ٱلۡأَحۡمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مِنۡ أَمۡرِهِۦ يُسۡرٗا

Kuma waɗanda suka yanke* ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa. info

* Muddar idda ga wadda ta yanke ɗammãnin haila, sabõda tsũfa, watanni uku,kuma bã zã ta ƙãra kõme ba a kai. Wadda take akwai shakka a game da ita ga kõ akwai ciki kõ bãbu shi, to, zã ta yi iddar wattani uku kuma ta yi jiran watanni tara, watau ta yi watannin shekara, uku na idda, saurãn na fidda shakkãne. Haka ne hukuncin mai istihãla, watau jinin ciwo. Amma yãrinya mai shakkar ciki, sai ta zauna har shakka ta gushe. Yarinyar da ba ta fãra haila ba tana iddar wata uku. Bãbu bambanci a tsakãnin ɗiya da baiwa ga idda da watanni, amma ga idda ta tsarki, to, baiwã tana yin rabin na ɗiya ga saki da mutuwa.

التفاسير:

external-link copy
5 : 65

ذَٰلِكَ أَمۡرُ ٱللَّهِ أَنزَلَهُۥٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَيِّـَٔاتِهِۦ وَيُعۡظِمۡ لَهُۥٓ أَجۡرًا

Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sãkamako. info
التفاسير: