ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمهه‌ى هوساوى - ابوبكر جومى

شماره صفحه:close

external-link copy
36 : 28

فَلَمَّا جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا بَيِّنَٰتٖ قَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّفۡتَرٗى وَمَا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِيٓ ءَابَآئِنَا ٱلۡأَوَّلِينَ

To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko." info
التفاسير:

external-link copy
37 : 28

وَقَالَ مُوسَىٰ رَبِّيٓ أَعۡلَمُ بِمَن جَآءَ بِٱلۡهُدَىٰ مِنۡ عِندِهِۦ وَمَن تَكُونُ لَهُۥ عَٰقِبَةُ ٱلدَّارِۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّٰلِمُونَ

Kuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara." info
التفاسير:

external-link copy
38 : 28

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ مَا عَلِمۡتُ لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرِي فَأَوۡقِدۡ لِي يَٰهَٰمَٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجۡعَل لِّي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka* (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata." info

* Fir'auna ya fãra yin gasasshen tũbali da ake cewa ajurru, aka gina masa dõgon bene, ya hau samansa, ya harba kibiya ta tafi ama, ta kõmo da jini. Saĩ ya ce: "yã kashe Ubangijin Mũsa." Bayan haka sai benen ya karye guntu uku' guntu ɗaya ya fãɗa wa sõjansa, da yawa daga cikinsu suka mutu, guntu ɗaya kuma ya fãɗa a cikin ruwa, sauran guntu ɗaya ya fãɗa wa magina, suka mutu. Kuma cewar Fir'auna, "Lalle ne nĩ, inã zuton Mũsã daga maƙaryata," ya nũna girman kansa kawai ne ya hana shi ĩmãni, ba rashin gãnewa ba, sai dai kuma sun ga kamar bãbu Tãshin Ƙiyãma.

التفاسير:

external-link copy
39 : 28

وَٱسۡتَكۡبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُۥ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ إِلَيۡنَا لَا يُرۡجَعُونَ

Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 28

فَأَخَذۡنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلظَّٰلِمِينَ

Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance. info
التفاسير:

external-link copy
41 : 28

وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَئِمَّةٗ يَدۡعُونَ إِلَى ٱلنَّارِۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا يُنصَرُونَ

Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba. info
التفاسير:

external-link copy
42 : 28

وَأَتۡبَعۡنَٰهُمۡ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا لَعۡنَةٗۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ هُم مِّنَ ٱلۡمَقۡبُوحِينَ

Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu. info
التفاسير:

external-link copy
43 : 28

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ مِنۢ بَعۡدِ مَآ أَهۡلَكۡنَا ٱلۡقُرُونَ ٱلۡأُولَىٰ بَصَآئِرَ لِلنَّاسِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لَّعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ

Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa. info
التفاسير: