* Yãƙũbu ya umurci ɗiyansa su shiga garin, ta ƙõfõfi dabam- dabam, yanã nũna cewa yanã gudun kyawunsu da yawansu zai ja hankalin mutãne zuwa gare su. A cikin mutãne akwai mãsu kambun baka da mugun nufi kõ da yake Yãƙũba a cikin hãlin haka ya aza tawakkalinsa ga Allah. Ya yi abin da yake zaton alhħri ne, wanda bai saɓa wa sharĩ'a ba. Amma kuma yã yi haka ne a kan wani ilmi da Allah Ya sanar da shi cewa a wannan fitar tãsu ce Allah zai yi sanadin sãke sãduwarsu da Yũsufu, sabõda haka ya umurce su da su shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, dõmin mutum shi kaɗai yã fi sãmun dãmar ta'ammalin ganin mutãne da abũbuwa. Kuma ta yin haka, yanã tsammãnin waninsu zai ga Yũsufu.