আল-কোৰআনুল কাৰীমৰ অৰ্থানুবাদ - হাউছা অনুবাদ- আবু বকৰ গুম্মী

Al'burouj

external-link copy
1 : 85

وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡبُرُوجِ

Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 85

وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡمَوۡعُودِ

Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,* info

* Rãnar Ƙiyãma.

التفاسير:

external-link copy
3 : 85

وَشَاهِدٖ وَمَشۡهُودٖ

Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta* a cikinsa info

* Rãnar Arafa.

التفاسير:

external-link copy
4 : 85

قُتِلَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأُخۡدُودِ

An la'ani mutãnen rãmi.* info

* Mutãnen Najiran ne suka yi rãmi suka hũra wuta a ciki, dõmin su ƙõne wanda yã yi ĩmãni da addinin Masĩh Ĩsa dõmin su hana yãɗuwarsa. Suka umurci kõwane Musulmi ya jefa kansa a ciki, su kuma suna zazzaune suna kallo.

التفاسير:

external-link copy
5 : 85

ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلۡوَقُودِ

Wato wuta wadda aka hura. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 85

إِذۡ هُمۡ عَلَيۡهَا قُعُودٞ

A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 85

وَهُمۡ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ شُهُودٞ

Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 85

وَمَا نَقَمُواْ مِنۡهُمۡ إِلَّآ أَن يُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ

Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 85

ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 85

إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُواْ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَتُوبُواْ فَلَهُمۡ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمۡ عَذَابُ ٱلۡحَرِيقِ

Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 85

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡكَبِيرُ

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 85

إِنَّ بَطۡشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ

Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 85

إِنَّهُۥ هُوَ يُبۡدِئُ وَيُعِيدُ

Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa). info
التفاسير:

external-link copy
14 : 85

وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلۡوَدُودُ

Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 85

ذُو ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡمَجِيدُ

Mai Al'arshi mai girma info
التفاسير:

external-link copy
16 : 85

فَعَّالٞ لِّمَا يُرِيدُ

Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 85

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡجُنُودِ

Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 85

فِرۡعَوۡنَ وَثَمُودَ

Fir'auna da samũdãwa? info
التفاسير:

external-link copy
19 : 85

بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي تَكۡذِيبٖ

Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 85

وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطُۢ

Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa). info
التفاسير:

external-link copy
21 : 85

بَلۡ هُوَ قُرۡءَانٞ مَّجِيدٞ

Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 85

فِي لَوۡحٖ مَّحۡفُوظِۭ

A cikin Allo tsararre. info
التفاسير: