আল-কোৰআনুল কাৰীমৰ অৰ্থানুবাদ - হাউছা অনুবাদ- আবু বকৰ গুম্মী

পৃষ্ঠা নং:close

external-link copy
53 : 8

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ لَمۡ يَكُ مُغَيِّرٗا نِّعۡمَةً أَنۡعَمَهَا عَلَىٰ قَوۡمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُواْ مَا بِأَنفُسِهِمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

"Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya ni'imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu, kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ, Masani." info
التفاسير:

external-link copy
54 : 8

كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ فَأَهۡلَكۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡ وَأَغۡرَقۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَۚ وَكُلّٞ كَانُواْ ظَٰلِمِينَ

Kamar al'adar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu Zãlunci. info
التفاسير:

external-link copy
55 : 8

إِنَّ شَرَّ ٱلدَّوَآبِّ عِندَ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Lalle mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne waɗanda suka kãfirta, sa'an nan bã zã su yi ĩmãni ba. info
التفاسير:

external-link copy
56 : 8

ٱلَّذِينَ عَٰهَدتَّ مِنۡهُمۡ ثُمَّ يَنقُضُونَ عَهۡدَهُمۡ فِي كُلِّ مَرَّةٖ وَهُمۡ لَا يَتَّقُونَ

Waɗanda ka yi ƙullin alkawari da su, daga gare su, sa'an nan kuma sunã warwarewar alkawarinsu a kõwane lõkaci kuma sũ, bã su yin taƙawa. info
التفاسير:

external-link copy
57 : 8

فَإِمَّا تَثۡقَفَنَّهُمۡ فِي ٱلۡحَرۡبِ فَشَرِّدۡ بِهِم مَّنۡ خَلۡفَهُمۡ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ

To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre* waɗanda suke a bãyansu, game da su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa. info

* Wãtau a kashe waɗanda aka kãma dõmin saura su gani su ji tsõro.

التفاسير:

external-link copy
58 : 8

وَإِمَّا تَخَافَنَّ مِن قَوۡمٍ خِيَانَةٗ فَٱنۢبِذۡ إِلَيۡهِمۡ عَلَىٰ سَوَآءٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡخَآئِنِينَ

Kuma in ka ji tsõron wata yaudara daga wasu mutãne, to, ka jẽfar da alkawarin, zuwa gare su, a kan daidaita: Lalle ne Allah, bã Ya son mayaudara. info
التفاسير:

external-link copy
59 : 8

وَلَا يَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ سَبَقُوٓاْۚ إِنَّهُمۡ لَا يُعۡجِزُونَ

Kuma waɗanda suka kãfirta kada su yi zaton sun tsẽre: Lalle ne sũ, bã zã su gãgara ba. info
التفاسير:

external-link copy
60 : 8

وَأَعِدُّواْ لَهُم مَّا ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن قُوَّةٖ وَمِن رِّبَاطِ ٱلۡخَيۡلِ تُرۡهِبُونَ بِهِۦ عَدُوَّ ٱللَّهِ وَعَدُوَّكُمۡ وَءَاخَرِينَ مِن دُونِهِمۡ لَا تَعۡلَمُونَهُمُ ٱللَّهُ يَعۡلَمُهُمۡۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِن شَيۡءٖ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ يُوَفَّ إِلَيۡكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تُظۡلَمُونَ

Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi,* kuma da ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba a zãluntar ku. info

* Tattali daga wani ƙarfi, ya haɗa dukkan abin da zai yiwu a yi yãƙin abõkin gãba da shi. A yanzu daga bindiga da abin da yake sama da ita, shi ne zã a yi tattali.

التفاسير:

external-link copy
61 : 8

۞ وَإِن جَنَحُواْ لِلسَّلۡمِ فَٱجۡنَحۡ لَهَا وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani. info
التفاسير: