* Asalin mubãya'a daga bai'u ne, watau ciniki, wanda ya yi mubãya'a ga Limãmin Musulmi kamar yã yi ciniki ne yã sayar da ransa, dõmin ya karɓi Aljanna daga Allah a Rãnar Ƙiyãma. Mubãya'a ta farko,ita ce wadda aka yi wa Annabi a Hudaibiyya wani ɗan gari ne kusa da Makka a hanyar Jidda, tafiyar kwana ɗaya. An ce tanã cikin Hurumi, waɗansu sun ce bã ta cikinsa.
* Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya yi nufin tafiya Makka dõmin ya yi Umra sabõda mafarkin da ya yi cewa yã ga ya shiga Makka shi da Sahabbansa, sunã mãsu yin aski da saisaye na ibãda, sai ya ce wa ƙauyãwan da ke gefen Madina su fita tãre da shi dõmin kada Ƙuraishãwa su fãɗa shi da yãƙi,su tsare shi daga Ɗãkin. Kuma ya yi harama ya kõra hadaya dõmin mutãne su san bã yãƙi yake nufi ba. Sai waɗansu mãsu yawa daga ƙauyãwa suka yi nauyin fita, sukayi zamansu kuma suka ce: "Zai tafi zuwa ga mutãnen da suka yãƙe shi a tsakar gidansa a Madĩna, suka kashe Sahabbansa. Ba zã mu bĩ shi ba dõmin mu halaka kanmu.".
* A bãyan sulhun Hudaibiyya Allah Ya yi wa Annabi alkawarin zai buɗe masa Haibara ya sãmi ganĩma mai yawa, amma kuma kada ya bari ƙauyãwan da aka nema su fita zuwa Makka, suka ƙi su fita tãre da shi.