আল-কোৰআনুল কাৰীমৰ অৰ্থানুবাদ - হাউছা অনুবাদ- আবু বকৰ গুম্মী

পৃষ্ঠা নং:close

external-link copy
13 : 20

وَأَنَا ٱخۡتَرۡتُكَ فَٱسۡتَمِعۡ لِمَا يُوحَىٰٓ

"Kuma Nĩ nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi." info
التفاسير:

external-link copy
14 : 20

إِنَّنِيٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدۡنِي وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكۡرِيٓ

"Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni." info
التفاسير:

external-link copy
15 : 20

إِنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٌ أَكَادُ أُخۡفِيهَا لِتُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا تَسۡعَىٰ

"Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa." info
التفاسير:

external-link copy
16 : 20

فَلَا يَصُدَّنَّكَ عَنۡهَا مَن لَّا يُؤۡمِنُ بِهَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ فَتَرۡدَىٰ

"Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka." info
التفاسير:

external-link copy
17 : 20

وَمَا تِلۡكَ بِيَمِينِكَ يَٰمُوسَىٰ

"Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!" info
التفاسير:

external-link copy
18 : 20

قَالَ هِيَ عَصَايَ أَتَوَكَّؤُاْ عَلَيۡهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَىٰ غَنَمِي وَلِيَ فِيهَا مَـَٔارِبُ أُخۡرَىٰ

Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci* na dabam a gare ta." info

* Amfãnõnin sanda: Anã riƙon alkĩbla a cikin daji ta zama sitra, anã dõgara a kanta sabõda gajiya kõ rauni. Lĩmãmin Juma'a na dõgara a kanta a lõkacin huɗuba anã fita da ita a cikin ruwan sama anã dõgara a kanta, anã dũkan iyãli da ita dõmin ladabtarwa. A cikin wani Hadĩsi Annabi ya ce: "Ka rãtaye sandarka inda iyãlinka suke ganin ta." Riƙon sanda na sanya farkawa gabarin dũniya, watau mai ita ya zama a cikin hãlin tafiya.

التفاسير:

external-link copy
19 : 20

قَالَ أَلۡقِهَا يَٰمُوسَىٰ

Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!" info
التفاسير:

external-link copy
20 : 20

فَأَلۡقَىٰهَا فَإِذَا هِيَ حَيَّةٞ تَسۡعَىٰ

Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 20

قَالَ خُذۡهَا وَلَا تَخَفۡۖ سَنُعِيدُهَا سِيرَتَهَا ٱلۡأُولَىٰ

Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko." info
التفاسير:

external-link copy
22 : 20

وَٱضۡمُمۡ يَدَكَ إِلَىٰ جَنَاحِكَ تَخۡرُجۡ بَيۡضَآءَ مِنۡ غَيۡرِ سُوٓءٍ ءَايَةً أُخۡرَىٰ

"Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam." info
التفاسير:

external-link copy
23 : 20

لِنُرِيَكَ مِنۡ ءَايَٰتِنَا ٱلۡكُبۡرَى

"Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyin Mu manya." info
التفاسير:

external-link copy
24 : 20

ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ

"Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)." info
التفاسير:

external-link copy
25 : 20

قَالَ رَبِّ ٱشۡرَحۡ لِي صَدۡرِي

Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa* mini, ƙirjĩna. info

* Ma'anar buɗa ƙirji, shine a sanya masa haƙuri.".

التفاسير:

external-link copy
26 : 20

وَيَسِّرۡ لِيٓ أَمۡرِي

kuma ka sawwake mun Al'amari na info
التفاسير:

external-link copy
27 : 20

وَٱحۡلُلۡ عُقۡدَةٗ مِّن لِّسَانِي

"Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna." info
التفاسير:

external-link copy
28 : 20

يَفۡقَهُواْ قَوۡلِي

"Su fahimci maganãta." info
التفاسير:

external-link copy
29 : 20

وَٱجۡعَل لِّي وَزِيرٗا مِّنۡ أَهۡلِي

"Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena." info
التفاسير:

external-link copy
30 : 20

هَٰرُونَ أَخِي

"Hãrũna ɗan uwana." info
التفاسير:

external-link copy
31 : 20

ٱشۡدُدۡ بِهِۦٓ أَزۡرِي

"Ka ƙarfafa halittata da shi." info
التفاسير:

external-link copy
32 : 20

وَأَشۡرِكۡهُ فِيٓ أَمۡرِي

"Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina." info
التفاسير:

external-link copy
33 : 20

كَيۡ نُسَبِّحَكَ كَثِيرٗا

"Dõmin mu tsarkake Ka da yawa." info
التفاسير:

external-link copy
34 : 20

وَنَذۡكُرَكَ كَثِيرًا

"Kuma mu tuna Ka da yawa." info
التفاسير:

external-link copy
35 : 20

إِنَّكَ كُنتَ بِنَا بَصِيرٗا

"Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu." info
التفاسير:

external-link copy
36 : 20

قَالَ قَدۡ أُوتِيتَ سُؤۡلَكَ يَٰمُوسَىٰ

Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!" info
التفاسير:

external-link copy
37 : 20

وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَيۡكَ مَرَّةً أُخۡرَىٰٓ

"Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam." info
التفاسير: